Sunday, 13 March 2022

AMFANONIN ZUMUNCI GA DANGI





AMFANONIN ZUMUNCI GA DANGI
منافع صلة الرحم
1. Allah yana farin ciki da mai sada zumunci.
رضا الله تعالي
2. Zumunci na haifar da farin ciki ga mai yin sa.
ادخال السرور علي المومن مع الفرح.
3. Mala'iku na farin ciki ga mai sada zumunci.
فرح الملاءكة.
4. Mai sada zumunci na samun yabo da godiya.
حسن الثناء.
5. Shaiɗan na baƙin ciki ga mai zumunci.
ادخل الغم علي ابليس.
6. Allah na ƙarawa mai sada zumunci tsawon rayuwa.
زيادة في العمر.
7. Allah na sanya albarka a cikin dukiyar mai sada zumunci.
بركة في الرزق.
8. Sada zumunci na sanya farin ciki yayin mutuwa. 
سرور لاموات.
9. Yana samun lada bayan mutuwa saboda 'yan uwa za su riƙa tunawa da shi suna masa addu'a.
زيادة الاجر بعد وفاته لان الاقربين يدعون له.
10. Sada zumunci na ƙara soyayya.
بصلة الرحم تزداد المحبة.
11. Sada zumunci na sanya ƙauna.
تقوي اواصر الالفة بين افراد الاسرة.
12. Ta hanyar sada zumunci ne dangi ke sanin junansu.
بها يتعارف افراد الاسرة.
13. Zumunci na sanya farin ciki da nishaɗi.
تدخل الفرح والسرور في قلوب.
14. Sada zumunci na sanya danƙon ƙauna tsakanin 'yan uwa.
وتقوى العلاقة الاسرية.
15. Sada zumunci na gadar da wanzuwar iyali.
صلة الرحم تحفظ النسل.
16. Sadar da zumunci na sanya mutum ya sami sakamako mai ƙyau wajen Allah.
تسير الحساب امام الله.
17. Sada zumunta na kankare zunubi.
تكفر الذنوب والخطايا.
18. Sada zumunci na zamowa dukiya cikin Aljanna.
صلة الرحم من كنز الجنة.
19. Sada zumunci na ɗaya daga cikin manyan ayyuka na gari.
هىي من أفضل الفضاءل.
Allah ya datar da mu. Ya sanya mu zama masu kusanci ga 'yan uwa da abokan arziƙi.
 Dan Allah inabukatar kayimin addu,a Allah  yasa ingama da duniya lafiya yasa intsallake kyc wassalam jabir mukhtar bello
Copying

SHIN MECECE MUTUWA? (01)





SHIN MECECE MUTUWA? (01)

Mutuwa ita ce rabuwar ruhi da jiki. Wato da zarar ruhinka ya fita daga jikinka to ka mutu kenan. Mutuwa ita ce fitarka daga wani halin zuwa ga wani.. Kuma ita ce fita daga wannan gidan (duniya) zuwa ga wani gidan (lahira). 

Allah da kansa yace Mutuwa Musibah ce.. Acikin littafinsa mai girma inda yake cewa :

"IDAN KUNA TAFIYA A DORON QASA SAI MUSIBAR MUTUWA TA SAMEKU...".

Hakika lallai mutuwa Musibah ce. Amma musibar da tafi ta girma ita ce : GAFALA (WATO RAFKANA) DAGA BARIN AMBATONTA.. Wato Mantawa da tunanin mutuwar. Da kuma rashin yin kyakkyawan tanadin guzuri saboda ranar zuwanta. 

Hakika guzuri ya kamaci mai tafiya. Shi yasa Annabinmu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wa'azantar damu da irin wa'azin nan mai saurin tsinka zukata, Mai sanya mutum yayi ma kansa hisabi. Kuma yace : "KU YAWAITA AMBATON MAI YANKE JIN-DADI". WATO MUTUWA.

Mutuwa tana zuwa ne babu zato babu tsammani (Bagtatan). Dani mai rubutun, da ku masu karatun nan babu wanda yasan yaushe zai, mutu ? A wanne waje zai, mutu? Da yaya zai mutu? Kuma menene ajalinsa?. 

Wannan ita ce babbar tambayar da bata da amsa.. Kuma babu wani daga cikin mutane wanda ya santa balle ya gaya maka.. Shima bai san tasa ba, balle yasan ta wani. 

Allah yana cewa : "ALLAH AWAJENSA NE SANIN ALQIYAMAH YAKE, KUMA SHI KE SAUKAR DA GIZA-GIZAI KUMA YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA. 

"BABU WATA RAI WACCE TASAN ABINDA ZATA TSUWURWURTA GOBE, KUMA BABU WATA RAI DA TASAN AWACCE QASA NE ZATA MUTU".

Hakika mantuwa ko rafkanuwa daga tunanin Mutuwa da 'dacin nan nata, da Kwanciyar Qabari da duhun nan nasa, Da tambayoyin nan na Mala'iku da tsananinta, da ranar Alqiyamah da Tashin hankalin nan nata, da hawan siradi da kaifin nan nasa, Mantuwa daga ambato ko tunanin wadannan yakan sanya zuciya ta bushe har ma alfasha da 'barna su bayyana acikin doron Qasa da teku.. 

Ka sani cewar idan kai mai tuna mutuwa ne, to zaka kasance mai tanadin guzuri domin zuwanta..

Shin yaya sallarka take? Shin kana yinta akan lokacinta, tare da Ikhlasi da tsoron Allah? Shin kana da ilimin sanin tsarki da alwala da hukunce-hukuncen Salla?. In baka dashi mai ya hanaka ka nema?? -- Neman duniya ko? 

Yaya azuminka yake? Shin kana tsaftace idanunka da harshenka ayayin da kake azumi? Shin kana kiyayesu daga kallon haramun, ko furta kalmomon haramun? Ko tunanin aikata sa'bon Allah??.

Shin yaya bin iyayenka yake? Shin kana basu hakkinsu kamar yadda ya dace? Baka 'bata musu rai, baka yi musu tairin kai da girman kai? Shin baka fifita matarka ko abokanka akansu?. 

Yaya sadar da zumuncinka yake? Shin kana hakuri da wautar 'yan uwanka? Shin kana basu hakkinsu? Kana kyautata musu? Kana ziyartarsu?. Ko ko ka biye ma zuciya kana rama mugunta da mugunta?. 

Yaya Mu'amalarka da mutane take? Shin kana sakin fuska ga dukkan Musulmai? Shin kana girmama kowa, kana zaman lafiya da kowa? Shin kana kwatanta adalci da gaskiya da rikon amana acikin kowacce harka ta cikin gidanka da wajen aikinka ko kasuwarka?.

Yaya dukiyarka take? Yaya abincinka da abin shanka yake? Ka tabbatar kan cin halal dinka kana kiyayewa daga haram?. 

Idan akwai matsala yi kokari ka gyara.. Domin mutuwa tana daf da kai.. Mala'ikan mutuwa kullum yana shafa kanka sau saba'in.. Zai iya chafke ruhinka duk sanda aka umurceshi.. 

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU



KHAMSUNA HADISI• •HADISI NA 19•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada kuci da hannun hagu, domin shaiɗan ne keci da hannun hagu.

[Ibn majah]

DARASI:

Ma'ana haramun ne cin wani abinci da hannun hagu.

kuma cin abinci ko sha da hagu yana iya jawowa mutum karɓar sakamakonsa da hagu a ranar Alƙiyama.

Ba ɗabi'ar mumini bace cin abu da hannun hagu.

•HADISI NA 20•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada ɗayanku yasha abinsha a tsaye.

[Muslim].

DARASI:

Haramun ne shan abinsha a tsaye ko cin wani abu a tsaye.

Saidai mutum ya zauna ko a tsuguna.

Duk wanda yake shan abun sha a tsaye to baya daga cikin mabiya umarnin ALLAH da Manzonsa {s.a.w}.

Ansamu a hadisi cewa Manzon ALLAH {s.a.w} ya sha abin-sha a tsaye, amma idan aka duba waɗannan hadisai sosai za'asamu akwai dalili dayasa ya aikata hakan.

Saboda kiyayewa shine abu mafi alkhairi.

•HADISI NA 21•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada ɗayanku yayi tafiya da takalmi kafa ɗaya.

[Bukhari da Muslim]

DARASI:

Haramun ne mutum yayi tafiya da takalmi guda ɗaya, sai dai ko ya cire dukka ko kuma ya saka dukka.

Saboda idan takalmin ɗayanku ya tsinke to ya cire dukka kada yayi tafiya acikin takalmi guda ɗaya.

Duk mai aikata haka zai sami kansa acikin fushin ALLAH, kuma sami kansa cikin mummunan hali saboda rashin bin Umarnin ALLAH da manzonsa {s.a.w}.

ALLAH shine mafi sani.

ALLAH kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya.
Ameen...


Friday, 11 March 2022

KARATUN TAFIN HANNU 1 AND 14




ASSALAMUALAIKUM YAN UWA ALMAJIRAI MASOYA ANNABI MUHAMMADU S A W MUNA MUKU BARKA DA WANNAN LOKACI YAU  ZAMU CIGABA DA KARATUN TAFIN HANNU 👇🤳🏦 


 

SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNAH




SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNAH 

👉 1. Abubakar Assiddik.
👉 2. Umar Dan Khaddab.
👉 3. Usman Dan Affan.
👉 4. Aliyu Dan Abi Dalib.
👉 5. Dalha Dan Abaidullahi.
👉 6. Zubairu Dan Awwam.
👉 7. Abu Ubaida Dan Jarrah.
👉 8. Abdurrahman Dan Aufu.
👉 9. Sa'adu Dan Abi Wakkas.
👉 10. Sa'idu Dan Zaid.

SHIKA SHIKAN MUSULUNCI GUDA BIYAR 

👉 1. Tauhidi.
👉 2. Sallah.
👉 3. Azumi.
👉 4. Zakkah.
👉 5. Hajji.

SUNAYEN WATANNIN MUSULUNCI : 

👉 1. Almuharram.
👉 2. Safar.
👉 3. Rabi'ul Awwal.
👉 4. Rabi'ul Sani.
👉 5. Jumadal Ula.
👉 6. Jumadal Akhirah.
👉 7. Rajab.
👉 8. Sha'aban.
👉 9. Ramadhan.
👉 10. Shawwal.
👉 11. Zulkidah.
👉 12. Zulhijji.

Ya Allah duk wanda ya taimaka wajen yada wanan ilmin don wasu su amfana; 
Ya Allah ka haskaka rayuwarsa da annurinka, 
Kasa yayi kyakkyawar karshe,
Ka sashi a inuwar Al'arshenka ranar  Alkiyama,
Kuma ka shayar da shi ruwan Alkausara,
Ya Allah ka sa mu  ziyarci juna a gidan Aljannah,
Amin Summa Amin 👏🏻👏👏👏👏👏👏👏

RANAR ALKIYAMA TSAYAWA GABAN ALLAH




Ranar Al Qiyama Kowane Mutum Idan yatashi Abinda yake Qira: Nafsi Nafsi, Annabawa Da Manzanni= Nafsi Nafsi, Iyaye Da Yara= Nafsi Nafsi, Mata Da Maza= Nafsi Nafsi A ranar Shugaba Dayane Shine Annabi Muhammad Rasulullahi {S.a.w} Farkon Tashi Zaice Aina Ummati Aina Ummati Allahu Akabar 'Yan Uwa Kutuna fah yana Da Dangi Amma Daya Tashi Baice Ina Dangi Naba Sai Yace Ina Al'ummata, 'Yan Uwa ko Dan Wannan Bama So Annabi Ba 'Yan Uwa Dan Qaunar Ka/Ki Da Annabi Ka Tura Wannan Zuwa Grp 3 Ko Mutane 3 Ya Allah Ka Samu A Cetan Annabi Muhammadu {S.a.w}. Allah kasa mudace
ALBAKACIN ANNABI S,A,W,   ka tsaya KAKARANTA 
Ya allah ka kare duk wani musulmi daga sharrin.🙏

•Zina
•Luwadi
•Madigo
•Istimina'i
•Sata
•Zalunci
•Munafurci
•Qunchi
•Bashi
•Hasda
•Keta
•Zulama
•Talauchin Duniya da Lahira.

Don alfarmar fiyeyyen halitta Annabi (S,A,W) kadaure kayi share zuwa groups (5)🙏
🔗
🔗 

Ya Allah Ka Karawa Duk wani Musulmin Duniya.

•Lafiya
•Hakuri
•Juriya
•Lafiya
•Karfin imani
•Hankali da Tunani mai kyau
•Mace tagari
•Minji na Gari
•'Ya'ya Na Gari
•Abokan Zama na Kirki
•Arzuki Mai Amfani
•Wadatar Zuci
•Ya Allah Karufawa Duk Wanda Ya
Karanta Wannan Sako Yayi share a groups Yace Ameen
Asiri Duniya da Lahira.

don Allah ☝️ kadaure kayi share zuwa groups 5 👌

SIRRIN BARHATIHIN NA ISMUL AZIM MAI GIRMA




SIRRIN BARHATIHIN NA ISMUL AZIM KADA KA BAWA WANI WANNAN SIRRIN SAI DANKA WANDA YAYI MAKA HIDIMA  SIRRI NE DA AKE BOYE SHI SABODA GIRMAN SHI


 



 

MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:-

MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:- "Bushewar Zuciya, Itace Mafi Girma a Cikin Bala'i Bayan Kafirci. Akwai Ayyuka Guda 24 Dake Busar Da Zuciya, Wanda SHARI'A Bata Yarda Da Su Ba, 'DARIKA Bata Yarda Dasu Ba, Hakama HAQIQA Bata Yarda Dasu Ba Sune Kamar Haka:- 1 - Mutum Ya Tsaya Akan Zunubi Guda Daya, Yayi Tayi Yana Maimaitawa. 2 - Tsawon Buri, Mutum Ya Zama Bai Wadata Da Abinda ALLAH Ya Bashi Ba. 3 - Yawan Fushi, Ba Akan Tafarkin ALLAH Ba. 4 - Musulmi Ya Riqe Dan'uwansa Musulmi a Zuciya. 5 - Son Duniya Kota Halin Yaya. 6 - Son Girma, Cikin Kowane Hali. 7 - Katsalandan a Harkar Da Ba Ruwanka a Ciki. 8 - Yawan Dariya, Mutum Ya Zama Kamar Wawa. 9 - Yawan Zolayar Mutane. 10 - Jindadi Saboda Abin Duniya, Har Kamanta Da ALLAH Saboda Farin Ciki. 11 - Baqin Ciki, Yayin Da Jindadi Ya Zo Ya Koma. 12 - Gafala Ga Barin Zikirin ALLAH. 13 - Rafkana Ga Barin Tunanin Lahira. 14 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Wuta. 15 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Aljannah. 16 - Yawan Yin Firar Banza. 17 - Yawan Yin Abota Da Wawaye. 18 - Da Yawan Cin Haram. 19 - Mugun Cin Abinci. 20 - Da Yawan Janyo Sha'awa. 21 - Yawan Barci 22 - Yawan Tunanin Banza 23 - Qarancin Ambaton ALLAH 24 - Jiji Da Kai KAJI BABBAN LIKITAN ZUCIYA MUN GODE SHEHU! ALLAH YA TSARE MANA ZUCIYOYINMU DAGA BUSHEWA AMEEEN.

Wednesday, 9 March 2022

MUWATTAH IMAM MALIK• •HADISI NA 36•



•MUWATTAH IMAM MALIK• 

•HADISI NA 36• 

Yahya ya bada Labari Daga Imam Malik (Rh) daga Yahya Ɗan Muhammad Ɗan Ɗahla'a daga Usman Ɗan Abdurrahaman cewa:

Babansa ya zantar dashi cewa: Shi yaji Sayyadi Umar Ɗan Khattab (RA) Yana yin Alwala fiyeda abinda yake ƙasan mayafinsa.

DARASI:

Wannan hadis yana mana nuni da halaccin yalwatawa acikin Alwala, wato mai Alwala zai iya wanke sama da gwiwar hannunsa koda yakai kusa da kafadarsa babu komai.

hakama ƙafarsa yana iya wankewa har izuwa ƙaurinsa.

• Yahya Yace: An Tambayi Imam Malik (Rh) Gameda wani mutum da yayi Alwala sai ya mance ya wanke fuska a maimakon ya fara da kurkure baki.

Ko kuma ya wanke hannayensa zuwa wuyan hannu wato zira'i kafin ya wanke fuskarsa, sai yace:

Yana mai amsa wananna tambaya:

Wanda ya wanke fuskarsa kafin kurkurar  baki, to ya kurkure bakin kawai ba sai ya sake wanke fuskarba.

Wanda kuma ya wanke hannunsa izuwa wuyan hannu kafin ya wanke fuskarsa, to ya wanke fuskarsa, sannan kuma ya sake wanke hannayensa zuwa wuyansu har sai ya wankesu bayan wanke fuska.

Idan ya kasance yana nan agun da yayi Alwala, ko kuma hakan ya farue a wajensa.

•Yahya Yace: Antambayi Imam Malik (Rh) Gameda mutumin da ya manta da kurkurar baki kuma ya manta da shaƙar ruwa a hancinsa bai tunaba har sai da yayi salla, sai yace:

Ba zai sake wata sallarba, kawai zai kurkure bakinsa ne, kuma ya shaƙi ruwa daga baya, Idan yana son yin sallah da wannan Alwalar.

ALLAH shine mafi sani.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmau baki ɗaya.
Ameen...

MATSALAR AZZARI YA KARE

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...