Friday, 11 March 2022

MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:-

MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:- "Bushewar Zuciya, Itace Mafi Girma a Cikin Bala'i Bayan Kafirci. Akwai Ayyuka Guda 24 Dake Busar Da Zuciya, Wanda SHARI'A Bata Yarda Da Su Ba, 'DARIKA Bata Yarda Dasu Ba, Hakama HAQIQA Bata Yarda Dasu Ba Sune Kamar Haka:- 1 - Mutum Ya Tsaya Akan Zunubi Guda Daya, Yayi Tayi Yana Maimaitawa. 2 - Tsawon Buri, Mutum Ya Zama Bai Wadata Da Abinda ALLAH Ya Bashi Ba. 3 - Yawan Fushi, Ba Akan Tafarkin ALLAH Ba. 4 - Musulmi Ya Riqe Dan'uwansa Musulmi a Zuciya. 5 - Son Duniya Kota Halin Yaya. 6 - Son Girma, Cikin Kowane Hali. 7 - Katsalandan a Harkar Da Ba Ruwanka a Ciki. 8 - Yawan Dariya, Mutum Ya Zama Kamar Wawa. 9 - Yawan Zolayar Mutane. 10 - Jindadi Saboda Abin Duniya, Har Kamanta Da ALLAH Saboda Farin Ciki. 11 - Baqin Ciki, Yayin Da Jindadi Ya Zo Ya Koma. 12 - Gafala Ga Barin Zikirin ALLAH. 13 - Rafkana Ga Barin Tunanin Lahira. 14 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Wuta. 15 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Aljannah. 16 - Yawan Yin Firar Banza. 17 - Yawan Yin Abota Da Wawaye. 18 - Da Yawan Cin Haram. 19 - Mugun Cin Abinci. 20 - Da Yawan Janyo Sha'awa. 21 - Yawan Barci 22 - Yawan Tunanin Banza 23 - Qarancin Ambaton ALLAH 24 - Jiji Da Kai KAJI BABBAN LIKITAN ZUCIYA MUN GODE SHEHU! ALLAH YA TSARE MANA ZUCIYOYINMU DAGA BUSHEWA AMEEEN.

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...