HANYOYIN DAƊEWA AKAN MACE
Wato yawan yin jima'i tsakanin ma'aurata na samar da wani yanayi na juriya da daɗewa kafin su kawo (fitar mani). yawan yin jima'i kamar yawan zuwa gidan motsa jiki ne, gwargwadon motsa jininka shine gwargwadon jure wahalar sa da zaka samu. Kuma wannan zai taimaka idan ɗaya daga cikinku baya azalo (withdrawal) domin yawan yin azalo na kara maka tsahon lokaci kafin ka kawo. shiyasa ma yake da kyau ku shawarci juna ya zama ana samar da azalo koda sau daya a sati.
DAUKAR LOKACI MAI TSAHO WAJEN WASANNI
Abinda mafi yawancin mutane suka dauka shine, aiwatar da wasanni kafin saduwa baya da wani tasiri. Sabanin hakan kuwa, yin wasanni kafin saduwa yana bada gudunmawa wajen samarda yanayi na annushuwa tsakanin ma'aurata, sannan yakan kara ma lokacin kasancewa taren tsaho. misali, idan kana daukar mintuna 3 ko 4 kayi komai ka gama tare da matarka ba tare da wasanni ba, idan aka aiwatar da wasanni za'a iya samar da mintuna 8 harma zuwa 10.
FITAR DA SABBIN HIKIMOMIN SADUWA
Idan ka daɗe tare da abokiyar zaman ka, ma'ana kuka kasance na wani lokaci mai tsaho, akwai bukatar ku samar da hikimomi da zasu dinga kara ma kasancewar ku armashi. idan ya zamana kun kasance akan wani salo guda ɗaya na saduwa ko yaushe, zaku kasance cikin gundura da neman canzawa. yana da kyau ku nemi shawarwari daga masana harkar jima'i dan samun sababbin salo da zasu kara muku dadewa tare.
JINKIRIN KAWOWA (INZALI)
Idan mutuminki yana da matsalar inzali da wuri, to ga hanyar da zaki kara matsa dogon zango. lokacin da yake kanki yana sukuwa, ya kusa zuwa gaba sai ki tsayar dashi ta hanyar zare azzakarin daga farjin ki, sai bayan kamar minti biyu sai ki maida masa shi ciki. ya zamana ana samun irin haka kamar sau uku ko huɗu a duk lokacin da kuke saduwa, wannan zai sa ya zama ya kara lokaci akan yadda ya saba, dalilin wannan lattin kawowar da kika masa gwaji akai.
MURZA KARKASHIN AZZAKARIN SA
Duk lokacin da kuke tare ki dinga murza can kasan burar sa, wato kusa da golayensa. hakan yana kara masa dadewa bai kawo ba ya kuma kara ma azzakarin karfi. saidai kada kiyi kuskuren lankwasar da azzakarin a wannan yanayin domin wannan na iya jawo masa lalacewar azzakarin
KE A SAMA SHI A KASA
Wato wannan position yana taimakawa sosai wajen dadewa ba'a kawo ba. domin a haka ko wannen ku zai kasance cikin nishadi ba tare da an taɓa wurare muhimmai ba da zasu sa akawo. yadda akeyi shine, kai zaka kwanta rigingine ita kuma ta hau kanka a zaune tana dan yin gaba da baya.
MAGANI
Daga karshe, yana da kyau ku nemi shawarar masana jima'i domin baku shawarwari da kuma nuna muku irin magungunan da zakuyi amfani dasu da shawo kan matsalar ku. Ba abu ne mai kyau ba ka dinga amfani da magani kawai ba tare da sahalewar likita ba domin zai iya cutar da kai ba tare da kasani ba.