Sunday, 13 March 2022

KHAMSUNA HADISI• •HADISI NA 19•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada kuci da hannun hagu, domin shaiɗan ne keci da hannun hagu.

[Ibn majah]

DARASI:

Ma'ana haramun ne cin wani abinci da hannun hagu.

kuma cin abinci ko sha da hagu yana iya jawowa mutum karɓar sakamakonsa da hagu a ranar Alƙiyama.

Ba ɗabi'ar mumini bace cin abu da hannun hagu.

•HADISI NA 20•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada ɗayanku yasha abinsha a tsaye.

[Muslim].

DARASI:

Haramun ne shan abinsha a tsaye ko cin wani abu a tsaye.

Saidai mutum ya zauna ko a tsuguna.

Duk wanda yake shan abun sha a tsaye to baya daga cikin mabiya umarnin ALLAH da Manzonsa {s.a.w}.

Ansamu a hadisi cewa Manzon ALLAH {s.a.w} ya sha abin-sha a tsaye, amma idan aka duba waɗannan hadisai sosai za'asamu akwai dalili dayasa ya aikata hakan.

Saboda kiyayewa shine abu mafi alkhairi.

•HADISI NA 21•

Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Kada ɗayanku yayi tafiya da takalmi kafa ɗaya.

[Bukhari da Muslim]

DARASI:

Haramun ne mutum yayi tafiya da takalmi guda ɗaya, sai dai ko ya cire dukka ko kuma ya saka dukka.

Saboda idan takalmin ɗayanku ya tsinke to ya cire dukka kada yayi tafiya acikin takalmi guda ɗaya.

Duk mai aikata haka zai sami kansa acikin fushin ALLAH, kuma sami kansa cikin mummunan hali saboda rashin bin Umarnin ALLAH da manzonsa {s.a.w}.

ALLAH shine mafi sani.

ALLAH kabamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya.
Ameen...


No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...