Wednesday, 9 March 2022

MUWATTAH IMAM MALIK• •HADISI NA 36•



•MUWATTAH IMAM MALIK• 

•HADISI NA 36• 

Yahya ya bada Labari Daga Imam Malik (Rh) daga Yahya Ɗan Muhammad Ɗan Ɗahla'a daga Usman Ɗan Abdurrahaman cewa:

Babansa ya zantar dashi cewa: Shi yaji Sayyadi Umar Ɗan Khattab (RA) Yana yin Alwala fiyeda abinda yake ƙasan mayafinsa.

DARASI:

Wannan hadis yana mana nuni da halaccin yalwatawa acikin Alwala, wato mai Alwala zai iya wanke sama da gwiwar hannunsa koda yakai kusa da kafadarsa babu komai.

hakama ƙafarsa yana iya wankewa har izuwa ƙaurinsa.

• Yahya Yace: An Tambayi Imam Malik (Rh) Gameda wani mutum da yayi Alwala sai ya mance ya wanke fuska a maimakon ya fara da kurkure baki.

Ko kuma ya wanke hannayensa zuwa wuyan hannu wato zira'i kafin ya wanke fuskarsa, sai yace:

Yana mai amsa wananna tambaya:

Wanda ya wanke fuskarsa kafin kurkurar  baki, to ya kurkure bakin kawai ba sai ya sake wanke fuskarba.

Wanda kuma ya wanke hannunsa izuwa wuyan hannu kafin ya wanke fuskarsa, to ya wanke fuskarsa, sannan kuma ya sake wanke hannayensa zuwa wuyansu har sai ya wankesu bayan wanke fuska.

Idan ya kasance yana nan agun da yayi Alwala, ko kuma hakan ya farue a wajensa.

•Yahya Yace: Antambayi Imam Malik (Rh) Gameda mutumin da ya manta da kurkurar baki kuma ya manta da shaƙar ruwa a hancinsa bai tunaba har sai da yayi salla, sai yace:

Ba zai sake wata sallarba, kawai zai kurkure bakinsa ne, kuma ya shaƙi ruwa daga baya, Idan yana son yin sallah da wannan Alwalar.

ALLAH shine mafi sani.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmau baki ɗaya.
Ameen...

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...