Sunday, 13 March 2022

AMFANONIN ZUMUNCI GA DANGI





AMFANONIN ZUMUNCI GA DANGI
منافع صلة الرحم
1. Allah yana farin ciki da mai sada zumunci.
رضا الله تعالي
2. Zumunci na haifar da farin ciki ga mai yin sa.
ادخال السرور علي المومن مع الفرح.
3. Mala'iku na farin ciki ga mai sada zumunci.
فرح الملاءكة.
4. Mai sada zumunci na samun yabo da godiya.
حسن الثناء.
5. Shaiɗan na baƙin ciki ga mai zumunci.
ادخل الغم علي ابليس.
6. Allah na ƙarawa mai sada zumunci tsawon rayuwa.
زيادة في العمر.
7. Allah na sanya albarka a cikin dukiyar mai sada zumunci.
بركة في الرزق.
8. Sada zumunci na sanya farin ciki yayin mutuwa. 
سرور لاموات.
9. Yana samun lada bayan mutuwa saboda 'yan uwa za su riƙa tunawa da shi suna masa addu'a.
زيادة الاجر بعد وفاته لان الاقربين يدعون له.
10. Sada zumunci na ƙara soyayya.
بصلة الرحم تزداد المحبة.
11. Sada zumunci na sanya ƙauna.
تقوي اواصر الالفة بين افراد الاسرة.
12. Ta hanyar sada zumunci ne dangi ke sanin junansu.
بها يتعارف افراد الاسرة.
13. Zumunci na sanya farin ciki da nishaɗi.
تدخل الفرح والسرور في قلوب.
14. Sada zumunci na sanya danƙon ƙauna tsakanin 'yan uwa.
وتقوى العلاقة الاسرية.
15. Sada zumunci na gadar da wanzuwar iyali.
صلة الرحم تحفظ النسل.
16. Sadar da zumunci na sanya mutum ya sami sakamako mai ƙyau wajen Allah.
تسير الحساب امام الله.
17. Sada zumunta na kankare zunubi.
تكفر الذنوب والخطايا.
18. Sada zumunci na zamowa dukiya cikin Aljanna.
صلة الرحم من كنز الجنة.
19. Sada zumunci na ɗaya daga cikin manyan ayyuka na gari.
هىي من أفضل الفضاءل.
Allah ya datar da mu. Ya sanya mu zama masu kusanci ga 'yan uwa da abokan arziƙi.
 Dan Allah inabukatar kayimin addu,a Allah  yasa ingama da duniya lafiya yasa intsallake kyc wassalam jabir mukhtar bello
Copying

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...