Friday, 11 March 2022
KARATUN TAFIN HANNU 1 AND 14
SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNAH
SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNAH
👉 1. Abubakar Assiddik.
👉 2. Umar Dan Khaddab.
👉 3. Usman Dan Affan.
👉 4. Aliyu Dan Abi Dalib.
👉 5. Dalha Dan Abaidullahi.
👉 6. Zubairu Dan Awwam.
👉 7. Abu Ubaida Dan Jarrah.
👉 8. Abdurrahman Dan Aufu.
👉 9. Sa'adu Dan Abi Wakkas.
👉 10. Sa'idu Dan Zaid.
SHIKA SHIKAN MUSULUNCI GUDA BIYAR
👉 1. Tauhidi.
👉 2. Sallah.
👉 3. Azumi.
👉 4. Zakkah.
👉 5. Hajji.
SUNAYEN WATANNIN MUSULUNCI :
👉 1. Almuharram.
👉 2. Safar.
👉 3. Rabi'ul Awwal.
👉 4. Rabi'ul Sani.
👉 5. Jumadal Ula.
👉 6. Jumadal Akhirah.
👉 7. Rajab.
👉 8. Sha'aban.
👉 9. Ramadhan.
👉 10. Shawwal.
👉 11. Zulkidah.
👉 12. Zulhijji.
Ya Allah duk wanda ya taimaka wajen yada wanan ilmin don wasu su amfana;
Ya Allah ka haskaka rayuwarsa da annurinka,
Kasa yayi kyakkyawar karshe,
Ka sashi a inuwar Al'arshenka ranar Alkiyama,
Kuma ka shayar da shi ruwan Alkausara,
Ya Allah ka sa mu ziyarci juna a gidan Aljannah,
Amin Summa Amin 👏🏻👏👏👏👏👏👏👏
RANAR ALKIYAMA TSAYAWA GABAN ALLAH
Ranar Al Qiyama Kowane Mutum Idan yatashi Abinda yake Qira: Nafsi Nafsi, Annabawa Da Manzanni= Nafsi Nafsi, Iyaye Da Yara= Nafsi Nafsi, Mata Da Maza= Nafsi Nafsi A ranar Shugaba Dayane Shine Annabi Muhammad Rasulullahi {S.a.w} Farkon Tashi Zaice Aina Ummati Aina Ummati Allahu Akabar 'Yan Uwa Kutuna fah yana Da Dangi Amma Daya Tashi Baice Ina Dangi Naba Sai Yace Ina Al'ummata, 'Yan Uwa ko Dan Wannan Bama So Annabi Ba 'Yan Uwa Dan Qaunar Ka/Ki Da Annabi Ka Tura Wannan Zuwa Grp 3 Ko Mutane 3 Ya Allah Ka Samu A Cetan Annabi Muhammadu {S.a.w}. Allah kasa mudace
ALBAKACIN ANNABI S,A,W, ka tsaya KAKARANTA
Ya allah ka kare duk wani musulmi daga sharrin.🙏
•Zina
•Luwadi
•Madigo
•Istimina'i
•Sata
•Zalunci
•Munafurci
•Qunchi
•Bashi
•Hasda
•Keta
•Zulama
•Talauchin Duniya da Lahira.
Don alfarmar fiyeyyen halitta Annabi (S,A,W) kadaure kayi share zuwa groups (5)🙏
🔗
🔗
Ya Allah Ka Karawa Duk wani Musulmin Duniya.
•Lafiya
•Hakuri
•Juriya
•Lafiya
•Karfin imani
•Hankali da Tunani mai kyau
•Mace tagari
•Minji na Gari
•'Ya'ya Na Gari
•Abokan Zama na Kirki
•Arzuki Mai Amfani
•Wadatar Zuci
•Ya Allah Karufawa Duk Wanda Ya
Karanta Wannan Sako Yayi share a groups Yace Ameen
Asiri Duniya da Lahira.
don Allah ☝️ kadaure kayi share zuwa groups 5 👌
SIRRIN BARHATIHIN NA ISMUL AZIM MAI GIRMA
MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:-
MAULANA SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yana Cewa:-
"Bushewar Zuciya, Itace Mafi Girma a Cikin Bala'i Bayan Kafirci. Akwai Ayyuka Guda 24 Dake Busar Da Zuciya, Wanda SHARI'A Bata Yarda Da Su Ba, 'DARIKA Bata Yarda Dasu Ba, Hakama HAQIQA Bata Yarda Dasu Ba Sune Kamar Haka:-
1 - Mutum Ya Tsaya Akan Zunubi Guda Daya, Yayi Tayi Yana Maimaitawa.
2 - Tsawon Buri, Mutum Ya Zama Bai Wadata Da Abinda ALLAH Ya Bashi Ba.
3 - Yawan Fushi, Ba Akan Tafarkin ALLAH Ba.
4 - Musulmi Ya Riqe Dan'uwansa Musulmi a Zuciya.
5 - Son Duniya Kota Halin Yaya.
6 - Son Girma, Cikin Kowane Hali.
7 - Katsalandan a Harkar Da Ba Ruwanka a Ciki.
8 - Yawan Dariya, Mutum Ya Zama Kamar Wawa.
9 - Yawan Zolayar Mutane.
10 - Jindadi Saboda Abin Duniya, Har Kamanta Da ALLAH Saboda Farin Ciki.
11 - Baqin Ciki, Yayin Da Jindadi Ya Zo Ya Koma.
12 - Gafala Ga Barin Zikirin ALLAH.
13 - Rafkana Ga Barin Tunanin Lahira.
14 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Wuta.
15 - Barin Yin Tunani Akan Sha'anin Aljannah.
16 - Yawan Yin Firar Banza.
17 - Yawan Yin Abota Da Wawaye.
18 - Da Yawan Cin Haram.
19 - Mugun Cin Abinci.
20 - Da Yawan Janyo Sha'awa.
21 - Yawan Barci
22 - Yawan Tunanin Banza
23 - Qarancin Ambaton ALLAH
24 - Jiji Da Kai
KAJI BABBAN LIKITAN ZUCIYA MUN GODE SHEHU!
ALLAH YA TSARE MANA ZUCIYOYINMU DAGA BUSHEWA AMEEEN.
Thursday, 10 March 2022
Wednesday, 9 March 2022
MUWATTAH IMAM MALIK• •HADISI NA 36•
•HADISI NA 36•
Yahya ya bada Labari Daga Imam Malik (Rh) daga Yahya Ɗan Muhammad Ɗan Ɗahla'a daga Usman Ɗan Abdurrahaman cewa:
Babansa ya zantar dashi cewa: Shi yaji Sayyadi Umar Ɗan Khattab (RA) Yana yin Alwala fiyeda abinda yake ƙasan mayafinsa.
DARASI:
Wannan hadis yana mana nuni da halaccin yalwatawa acikin Alwala, wato mai Alwala zai iya wanke sama da gwiwar hannunsa koda yakai kusa da kafadarsa babu komai.
hakama ƙafarsa yana iya wankewa har izuwa ƙaurinsa.
• Yahya Yace: An Tambayi Imam Malik (Rh) Gameda wani mutum da yayi Alwala sai ya mance ya wanke fuska a maimakon ya fara da kurkure baki.
Ko kuma ya wanke hannayensa zuwa wuyan hannu wato zira'i kafin ya wanke fuskarsa, sai yace:
Yana mai amsa wananna tambaya:
Wanda ya wanke fuskarsa kafin kurkurar baki, to ya kurkure bakin kawai ba sai ya sake wanke fuskarba.
Wanda kuma ya wanke hannunsa izuwa wuyan hannu kafin ya wanke fuskarsa, to ya wanke fuskarsa, sannan kuma ya sake wanke hannayensa zuwa wuyansu har sai ya wankesu bayan wanke fuska.
Idan ya kasance yana nan agun da yayi Alwala, ko kuma hakan ya farue a wajensa.
•Yahya Yace: Antambayi Imam Malik (Rh) Gameda mutumin da ya manta da kurkurar baki kuma ya manta da shaƙar ruwa a hancinsa bai tunaba har sai da yayi salla, sai yace:
Ba zai sake wata sallarba, kawai zai kurkure bakinsa ne, kuma ya shaƙi ruwa daga baya, Idan yana son yin sallah da wannan Alwalar.
ALLAH shine mafi sani.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmau baki ɗaya.
Ameen...
Tuesday, 8 March 2022
TARIHIN RAYUWAR MA,AIKI S,A,W (1)
Da Sunan Allah Mai rahama Mai Jin}ai, godiya ta tabbata ga Allah
Ubangijin halittu, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da zuriyarsa da sahabbansa da wa]anda suka biye musu
game da wa]an nan ~angarori, ina ro}on Allah Ya gafarta mana
Faru}i ya fassarasa da harshen Turanci daga harshen Turancia ]ab’i na
duk in da na ga haka, na kan ce: ban san in da mai littafi ya ciro wannan
(mustashiri}ai) suka samar na }arya dangane da rayuwar Muhammad
kawo fassarar wasu ayoyi da wasu hadisai wa]anda ba su inganta ba, wanda
fassara da harshen Turanci bai cika kawo in da ya ciro labari ba, don haka
kuma mayalwaci kamar wannan wadda ta ]auki nauyi wajen fassara shi
babu wani littafi na tarihin Manzon Allah(SAW) wanda ya ke da girma
na yi iya }o}ari na wajen gyarawa tare da kawo hadisai da suka inganta
da kyawon aiki har zuwa ranar sakamako.
Hajiya Daula Justice Muhammad Bello, ta yi tunanin wannan aiki ne, saboda
ba, amma na bayyana wasu daga cikinsu a ta}aice, kuma mai littafin ko mai
wan nan aiki Ya sanya Aljanna ce makomarmu.
takwas. Saboda haka Hajiya Daula Justice Muhammad Bello ta ]auki nauyin
Is’ha} Yunus Muhammad Tukur Almashgool Bauchi na fassara daga
kuskurenmu. Wannan littafi ya yalwata magana akan wasu ~angarori na
Muhammad Husain Haikal ya wallafa, kuma Sheikh Isma’il Raji A. Al
zuwa harshen Hausa. Kuma shi mai littafin da wanda ya yi wa littafin
~angarori da suka shafi tarihi. Musamman tarihin da Orientalists
fassara sun sami kansu wajen bin ra’ayin Orientalists musamman wajen
tarihi amma bai cika kawo labarin da aka sani cikin }ananun litattafan tarihi
(SAW) da abubuwa da suka shafi addininMusulunci, Allah Ya kar~a mana
Bayan haka ina fatar jama’ar Musulmai za su amfana da wannan littafi mai
muhimmanci Allah Ya saka mata da alherinSa. Kuma ina mi}a godiya ta ga
Wannan tarihi na wani littafi ne, wanda aka yi masa fassara zuwa harshen
ba, saboda haka mai karatu zai ga wasu ya}e-ya}e da Annabi (SAW) ya
aiwatar, bai ambace su ba. Haka kuma siffofin Annabi (SAW) bai ambace su
labari ba. Kuma na kanyi }o}arin kawo abin da ya tabbata gwargwadon iko,
saboda wannan fassara na yi shi ne cikin kwanaki arba’in daidai.
Muhammad Bello wadda ta ]auki nauyin fassarar wannan littafi, mai
Hausa, mai suna kamar haka: ‚The Life of Muhammad (SAW),‛ wanda Dr.
Daga }arshe ina mi}a godiya ta musamman ga Hajiya Daula Justice
muhimmanci, musamman masu magana da harshen Hausa. Saboda haka
fassara, kamar yadda mai karatu zai fahimci mafarin wannan fassara. Ni
harshen Turanci zuwa harshen Hausa, ta re da yin wasu gyare-gyare a wasu
Monday, 7 March 2022
Hijabi lulluɓin musulunci 🧕 _Gudummawar da musulunci ya bayar akan mace
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
⚜️⚜️⚜️Daga⚜️⚜️⚜️
🧕 Hijabi lulluɓin musulunci 🧕
_Gudummawar da musulunci ya bayar akan mace
📝 Ibraheem y. Ibraheem
Bismillahi rahmanirrahim
______
Haƙiƙa Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace‚ wanda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne‚ ta samu damar dawo da mutunci da haƙƙoƙinta da aka raba ta da su a ƙarƙashin zaluncin zamanin jahiliyyah na ƙarnoni da dama.Ta hakane musulunci ya ƙwato mata haƙoƙin ta yadda zata yi rayuwa cikin aminci da mutunci ƙarƙashin tsarin rayuwa mafificiya.
A karo na farko a tarihi‚ Mace ta samu damar amfana da haƙƙoƙinta na ɗan'adamtaka a ƙarƙashin tsari da dokoki irin na musulunci. An yaye wa mata‚ ƙangin zalunci‚ kana kuma at samu damar rayuwa a matsayin ɗan Adam mai mutunci‚ ɗaukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na miji. To amma fa dole ne wannan ’yanci ya kasance cikin iyakokin Allah.
Maɗaukakin sarki Wanda ya bawa Mace dama‚ kana kuma ya tsara Mata hanyar da za ta iya ba ba nata gudunmawar wajen gina ɗaukaka‚ ta tabbatar da gaskiya da kuma yaɗa alheri.
Yaɗa alheri ɗin kuwa shine ta kiyaye mutuncin ta wajen sanya yalwataccen sutura‚ da sanya kammalallen Hijabi‚ yanda musulunci ya ta nadar.... Mafarki da tatsuniya ba wajen waɗansu‚ idan har ba a ƙarfafa shi da ayoyi na Alqur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma mutanen gidansa {Ahlulbait} tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare su.
1_ A zamanin jahiliyyah‚ al’umma tana ganin mace wata bi-tsami‚ Wani abu na la’alana‚ ma tatta-irin muggan ayyukan shaiɗan‚ ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin Wata dabba ala halicce ta a yanayin ɗan adam. To amma ko da Alqur'ani yazo sai ya ƙaryata wannan ƙuduri‚ wanda saɓa wa gaskiya da kuma haƙiƙa.
Yaƙe yar uwa “sister” keda musulunci ya baki wannan gagarumin guduma wa miye naki bayyana tsaraicin ci ta hanyar amfani da sa gyale‚ ko tufafin da zai bayyana surar jikin ki‚ bayan kina aikata laifi ne mafi girma. Wato zunibi‚ yaci gaba da cewa namiji da mace irin ’yan tagwaye ne da suka fito daga maɓuɓɓuga da kuma manufa Guda.
“....ya ku mutane ! Ku bi Ubangijinku da taƙawa‚ wanda ya halicceku Daga Rai guda‚ kuma ya ya halitta‚ daga gareshi‚ ma’au-ransa‚ Kuma ya watsa gada gare su maza masu yawa da mata....”
Bayan bayyana matsayin mace a Rayuwa da kuma samuwar ɗan’adam a fili‚ Alqur'ani mai girma ya yi kakkausar suka Ga al’adar nan ta bisne ’ya’ya Mata da rai‚ wato wa’id {4}.....“kuma idan wanda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta‚ Saboda wani laifi ne aka kashe ta”?5Kana kuma kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga Aure har sai biya kuɗin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.
“....Ya ku waɗanda suka yi! Imani ba ya halatta a gare ku‚ ku gaji Mata a kan tilas. Kuma Kada ku hana su Aure domin ku tafi da shashen abin da kuka basu.....”6
Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulaƙanta su da mazaje suke yi. Don haka ne ma Alqur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske akan tausaya musu yayin mu’amala da su:
“.... kuma kuyi zamantakewa da su da alheri. Sa’an nan idan kun ƙi su‚ to‚ akwai tsammanin ku ƙi wani abu‚ Alhali kuwa Allah ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa.....”7
Ko da yake a da‚ talauci ma ya kan sa mutane su kashe ’ya’yansu musamman ma ’ya’yaye mata‚ Don haka Alqur'ani ya kawar da wannan al’amarin {daga kanta}:
In Sha Allah zamu dakata anan sai in Allah ta'ala ya kaimu sati na Gaba zamuci Gaba in Sha Allah. Abin da muka faɗa da-,dai Allah ya bamu ladansa, kurakurai Allah ya ya yafe mana. Ma assalawat ala Muhammad wa Ali Muhammad 🌹
اللهم على محمد وال محمد وعجل فرجهم وانصرجيوش المسلمين، سبحان ربك رب العزة عما يصفون وسلام على المرسلين والحمد لله رب العالمين، الفاتح
_WASIKA✍️ ZUWA GA MATASA👳🏻♀️ MASU AIKATA ISTIMNA'I🤏_*
*_WASIKA✍️ ZUWA GA MATASA👳🏻♀️ MASU AIKATA ISTIMNA'I🤏_*
*ma'anar ISTIMNA'I shine= fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba.*
Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suke samu a jikunansu sakamakon Istimna'i wato Masturbation. An kawo hujjoji
gamsassu daga Al-Qur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saw) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I, Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba.
Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena, bubban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin
wannan bala'in shine :
1. Kallon Fina-finan batsa.
2. Shiga shafukan internet na batsa.
3. Yin zantukan batsa tsakanin
saurayi da budurwa.
4. Kusantar zina ta hanyar kallo da
shafa, ko zance da dai sauransu.
Wasu kuma suna aikata hakan ne
dan gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi d'inma ZINAR bane!!
Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!!
1. MUTUWAR IDANU.
2. MUTUWAR AL'AURA.
3. CIWON BAYA.
4. BUGAWAR QIRJI.
5. RIKICEWAR TUNANI.
6. YAWAN MANTUWA.
7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI.
8. SAURIN INZALI.
9. SHAFAR ALJANU, ETC.
Wad'annan 'yan kad'an ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu a haka zai je ya tarar da hisabi.
DAN GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta, ku Qaurace ma duk wani abinda zai rinQa motsa muku sha'awa, idan
da hali kuje kuyi aure, idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi.
ALLAH YA SAUWAQE
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,
DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.
Manzon Allah (s.a.w) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA
DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"
*Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.*
*1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa."*
*2. Ina son in zama mafi arziQi a cikin mutane?*
*AMSA*
*sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci."*
*3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa."*
*4. Menene zai kare ni daga wuta?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi."*
*5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka."*
*6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah."*
*7. Ina son imanina ya zama ingantacce?*
*AMSA.*
*Sai ya ce "Ka gyara halayen ka."*
*8. Menene yake huce fushin Allah (S.W.T.)?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata ma 'yan uwa."*
*9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Mummunar hali shine rowa"*
*10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah?*
*AMSA*
*Sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah."*
*YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya.*
*INA ROQON MAI KARATU dan GIRMAN ALLAH DAN SON ANNABI kayi Qokari ka tura wani group d'in domin tunasarwa....🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Mungode*
Subscribe to:
Posts (Atom)
Domin samun mustajaba a kwana 9
Khatimin Allahu Muhammadu idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau 92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...

-
SIRRIN MALLAKAR MUTUM MACE KO NAMIJI Amman ajitsoron Allah kada kayishi don cuta ko San zuciya ga asirigaskiyane to ga asirin kamar haka ida...