Monday, 7 March 2022

Hijabi lulluɓin musulunci 🧕 _Gudummawar da musulunci ya bayar akan mace

🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦

⚜️⚜️⚜️Daga⚜️⚜️⚜️
🧕 Hijabi lulluɓin musulunci 🧕

_Gudummawar da musulunci ya bayar akan mace

📝 Ibraheem y. Ibraheem

Bismillahi rahmanirrahim
______
Haƙiƙa Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace‚ wanda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne‚ ta samu damar dawo da mutunci da haƙƙoƙinta da aka raba ta da su  a ƙarƙashin zaluncin zamanin jahiliyyah na ƙarnoni da dama.Ta hakane musulunci ya ƙwato mata haƙoƙin ta yadda zata yi rayuwa cikin aminci da mutunci ƙarƙashin tsarin rayuwa mafificiya.

A karo na farko a tarihi‚ Mace ta samu damar amfana da haƙƙoƙinta na ɗan'adamtaka a ƙarƙashin tsari da dokoki irin na musulunci. An yaye wa mata‚ ƙangin zalunci‚ kana kuma at samu damar rayuwa a matsayin ɗan Adam mai mutunci‚ ɗaukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na miji. To amma fa dole ne wannan  ’yanci ya kasance cikin iyakokin Allah.

Maɗaukakin sarki Wanda ya bawa Mace dama‚ kana kuma ya tsara Mata hanyar da za ta iya ba ba nata gudunmawar wajen gina ɗaukaka‚ ta tabbatar da gaskiya da kuma yaɗa alheri.

Yaɗa alheri ɗin kuwa shine ta kiyaye mutuncin ta wajen sanya yalwataccen sutura‚ da sanya kammalallen Hijabi‚ yanda musulunci ya ta nadar.... Mafarki da tatsuniya ba wajen waɗansu‚ idan har ba a ƙarfafa shi da ayoyi na Alqur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma mutanen gidansa {Ahlulbait} tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare su.

1_ A zamanin jahiliyyah‚ al’umma tana ganin mace wata bi-tsami‚ Wani abu na la’alana‚ ma tatta-irin muggan ayyukan shaiɗan‚ ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin Wata dabba ala halicce ta a yanayin ɗan adam. To amma ko da Alqur'ani yazo sai ya ƙaryata wannan ƙuduri‚ wanda saɓa wa gaskiya da kuma haƙiƙa.


Yaƙe yar uwa “sister” keda musulunci ya baki wannan gagarumin guduma wa miye naki bayyana tsaraicin ci ta hanyar amfani da sa gyale‚ ko tufafin da zai bayyana surar jikin ki‚ bayan kina aikata laifi ne mafi girma. Wato zunibi‚  yaci gaba da cewa namiji da mace irin ’yan tagwaye ne da suka fito daga maɓuɓɓuga da kuma manufa Guda.


“....ya ku mutane ! Ku bi Ubangijinku da taƙawa‚ wanda ya halicceku Daga Rai guda‚ kuma ya ya halitta‚ daga gareshi‚ ma’au-ransa‚ Kuma ya watsa gada gare su maza masu yawa da mata....”

Bayan bayyana matsayin mace a Rayuwa da kuma samuwar ɗan’adam a fili‚ Alqur'ani mai girma ya yi kakkausar suka Ga al’adar nan ta bisne ’ya’ya Mata da rai‚ wato wa’id {4}.....“kuma idan wanda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta‚ Saboda wani laifi ne aka kashe ta”?5Kana kuma kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga Aure har sai biya kuɗin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.


“....Ya ku waɗanda suka yi! Imani ba ya halatta a gare ku‚ ku gaji Mata a kan tilas. Kuma Kada ku hana su Aure domin ku tafi da shashen abin da kuka basu.....”6
Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulaƙanta su da mazaje suke yi. Don haka ne ma Alqur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske akan tausaya musu yayin mu’amala da su:

“.... kuma kuyi zamantakewa da su da alheri. Sa’an nan idan kun ƙi su‚ to‚ akwai tsammanin ku ƙi wani abu‚ Alhali kuwa Allah ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa.....”7
Ko da yake a da‚ talauci ma ya kan sa mutane su kashe ’ya’yansu musamman ma ’ya’yaye mata‚ Don haka Alqur'ani ya kawar da wannan al’amarin {daga kanta}:

In Sha Allah zamu dakata anan sai in Allah ta'ala ya kaimu sati na Gaba zamuci Gaba in Sha Allah. Abin da muka faɗa da-,dai Allah ya bamu ladansa, kurakurai Allah ya ya yafe mana. Ma assalawat ala Muhammad wa Ali Muhammad 🌹

اللهم على محمد وال محمد وعجل فرجهم وانصرجيوش المسلمين، سبحان ربك رب العزة عما يصفون وسلام على المرسلين والحمد لله رب العالمين، الفاتح


No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...