Sunday, 17 April 2022

ASÃRA MAFI GIRMA AWA

ASÃRA MAFI GIRMA AWATAN RAMADÃN
══════ ❁✿❁  ═══════
TA FARKO.
Kai Baka Tsaya Anyi Sallar-Tarãwĩhi da Kai ba, Kuma Kai Baka Tãshi Cikin Dare Kãyi Wata Ibdah ba, Sa'annan daga Cin Abincin Sahur, Ka Koma Bacci  Baka Sãmu Sallar-Asubahi ba.
LALLAI KA TAFKA ASÃRA
══════ ❁✿❁  ═══════
TA BIYU.
Ramadãn Na Neman Tafiya, Amma Har Yanzu Baka Sauke (ALQUR'ÃNI) Koda Sau ɗaya ba, Gãshi Kai Bãbu Ruwanka da Zuwu Jin Tafsĩri, Kã Kãsa Zuwa Kõda Na Yini ɗaya, Kuma 'Yar Sadakar Nan da Ake Kaiwa Masallaci Don Taimakon Marãyu, Ko Dabĩno da Ruwan Sanyi da Ake Kaiwa Don Sãmun Lãdan Masu Azumi, Babu Kai Aciki.
WANNAN BA 'KARAMAR ASÃRA BANE
══════ ❁✿❁  ═══════
TA UKU.
Ana Azumi Amma Kai Babu Ruwanka da Ambaton Allah, Sai Buga Game a Handset da Kallace-Kallencen Finãfinai da Gulmace-gulmace, da Musun-banza, Kuma alla-alla Kake yi Asha Ruwa Ka Kēta Alfarmar Daren Ramadãn da Sãbon Allah.
HM, ANYA KUWA!!!?
══════ ❁✿❁  ═══════
TA HU'DU.
Asãra Mafi Girma da Zaka  Tafka Shi Ne: A Sãmu Daren (Lailatul-Qadr) Yazo Ya Wuce Kana Shirga Bacci, Ko Kana  (Night-Browsing) Wanda Meyuwu wa, Wannnan Azumin Shĩne: Na 'Karshe A Rãyuwar ka Baka Sani ba.
ALLAH YA KYAUTA
══════ ❁✿❁  ═══════
#NASIHA
Kana da Sauran Lokacin da Zaka Rĩbata, Kwana (14) Ko (15) Suka Rage Maka, Wanda Acikin Su Ne (Lailatul-Qadr) Yake, Kada Kace Sai A Goman 'Karshe Zaka Neme Shi, A'ah, Ka Fara Rãya Dararen da Suka Rage Tun daga Yau Har Zuwa 'Karshen Ramadãn dan Sãmun Tabbacin Muwãfaqa da Lailatul-Qadr.
══════ ❁✿❁  ═══════
FÃTAN ALKHAIRI.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TAMBASIRUNIGERIALIMITED

MUTANE (7) ƳAN ALJANNAH 

Manzon Allah ﷺ, yace: *"mutane bakwai Allah yana inuwantar dasu a cikin inuwarsa a ranar da babu wata inuwa face sai inuwarsa"*
📒 Sahih Al-Bukhari (660)

👉🏿 *Shugaba mai adalci*, (shine wanda yake tabbatar da adalci a cikin talakawansa).

👉🏿 *Da matashi wanda ya rayu cikin bautar ubangijinsa (Allah).*

👉🏿 *Da mutumin da zuciyarsa ta ratayu (ta ƙullu ko ta shaƙu) da masallaci.*

👉🏿 *Da mutane biyun da suke soyayya domin Allah, suka haɗu dominsa, kuma suka rabu dominsa.*

👉🏿 *Da mutumin da mace ma'abociyar nasaba da kyawu ta nemeshi*, sai yace, *ni ina jin tsoron Allah.*

👉🏿 *Da mutumin da yayi sadaƙa, ya ɓoyeta*, hagunsa bata san me damansa ta bayar ba.

👉🏿 *Da mutumin da ya tuna Allah shi kaɗai, sai idaniyarsa ta zubar da ƙwalla, (hawaye).*
📒 Sahih Al-Bukhari (660)

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇https://t.me/TAMBASIRUNIGERIALIMITED








Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Friday, 15 April 2022

002 KARSHEN KASHI2TARIHIN ANNABI MUHAMMAD LADABI AKE KIRANSA BA AKIRAN S...

ALƘUR'ÃNI DA AZUMI SUNA YIN CETO

ALƘUR'ÃNI DA AZUMI SUNA YIN CETO.
-
"A ranar ƙiyamah alƙur'ani da azumi za suyi ceto ga bayi waɗanda suka kasance ma'abotansu ne a wannan duniyar, waɗanda suka ƙarar da rayuwarsu wajen yin ta'ammuli dasu a duniya" 
-
"Kowane daga cikinsu zai nemi Allah ta'ala ya bashi ceton dukkanin bawan da ya kasance yana neman kusanci da Allah dominsu, sai Allah buwayi ya basu ceton waɗannan bayin nan-take" 
-
"Ruwaya daga Abdullahi ɗan Amru, lallai Manzon Allah ﷺ, yace: azumi da alƙur'ani suna yin ceto ga bawa a ranar ƙiyamah, azumi zai ce: haƙiƙa ya ubangiji, ni na hanashi abinci, da sha'awa da rana, to ka bani ceton sa. alƙur'ani kuma sai yace: haƙiƙa na hanashi yin bacci da daddare, to ka bani ceton sa, sai yace: sai suyi ceton"
Ahmad ne ya ruwaito













Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Thursday, 14 April 2022

{{NASIHAR RANAR JUMMA'A}} (Hijirah 08-08- 1443)


Yau zamuja hankulan yan uwana musulmi kan lura da ayoyin Allah subahanahu wata'ala,,.  Dan uwa kasani cewa baka zama cikin mummunai inbaka tunani da lura kan ayoyin Allah,  yar uwa kisan dahaka,,

Meye anfanin zuciyar ka dan uwana da baka tuna Allah da ita, ta lura da ayoyin shi abankasa?  Meye anfanin zuciyar ki yar uwa dabakya tuna Allah da ita?   Meyesa bazakyi tunani ba,  

Kazauna kayi tunani dan uwana kaduba saman nan ya'akayi akaginata, kaduba kasan nan ya'akayi aka shimfidata, ka duba duwatsu da tekunan kaduba canjin dare da rana, kullun sai anyi dare kullun sai anyi rana toh dare da ranan nan suna zuwa kafin kai kuma zaka bar su, lalle yakamata kasan Allah inde kanada hankali, inde kina da lafiyayyen tunani yar uwata,,

Lura da dare da rana da jujjuya al'amura Allah yace ayace ga masu hankali, kai baka cikin masu hankalin ne,? Ke bakya ciki ne yar uwa?  Toh meye yasa bakwa tunawa,,. ?  Toh siffar bayin Allah mummunai suna lura da tunani akan ayoyin Allah,    sbd Allah bai haliice su don ayi wasa ba,,.   Bai halicce su ba don kawai ashentake amore,  a a ya halicce sune don suzame mana aya mubauta mishi shi kadai,, 
Allah yace>>

{{إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لَآيَاتٍ لِّأُولِي الْأَلْبَابِ

Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.

191
الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَٰذَا بَاطِلًا سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّار

Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: (suna cewa "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.}}

Toh yan uwa muke tunawa da lura da ayoyin Allah abankasa, domin samun tabbatuwar imani azukatan mu,,,  kar mudauki tunin turawa na  kawai Allah yakawomu duniyar nan don mushentake، muyi abunda mukaga dama,  duk ko wanda yabiyewa tunanin su, toh baizaiyi kishin Allah ba  , bazaiyi kishin Annabi s.a.w ba bazaiyi kishin Addinin musulunci da musulmai ba,,  saboda sun lalata mishi tunanin shi,,. Allah yarufamana asiri,,

Yaa Allah kasamu cikin bayinka masu tunawa da lura da Ayoyin ka, yaa ka gafarta mana mu da iyayenmu Baki daya,,yaa Allah ka albarka ci rayuwar mu, yaa Allah ka dauramu kan hanya madedeciya, ameen,




Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Monday, 11 April 2022

Abubuwa biyu basu da riba.

Abubuwa biyu basu da riba.
1 Soyayya ba Aure
2 Aure ba soyayya
.............................
Abubuwa biyu sukan dasa kauna.
1 Kyawawan dabi'u
2 Gaskiya
.............................
Abubuwa biyu kan rusa Abota.
1 Karya
2 Gulma ko rashin yadda
..............................
Abubuwa biyu kan kara kwarjini.
1 Rukon amana
2 Ibada
..............................
Abubuwa biyu nasa kunci.
1 Cin mutuncin manya
2 Kazafi
..............................
Abubuwa biyu nasa farin ciki.
1 Kyautatawa
2 hakuree
.............................
Abubuwa biyu nasa kusanci ga Allah.
1 karatun Qur'ani 
2 bin dokokinsa
.................,.............
Abubuwa biyu nasa shedan ya gujeka
1 Ambaton Allah
2 bujirewa son xuciya
..............................
Abubuwa biyu nasa ibada ta karbu
1 tauheedi
2 ikhlassi
..............................
Abubuwa biyu da Allah Yakeso
1 Kyautatawa
2 kyakkyawan hali
......,.......................
Abu biyune yasa na turo sakonnan
1 kasancewa musulmi
2 son da nakewa
musulunci
...........................
Abu biyu nakeso kayi in ka karanta
1 kayi aiki da shi
2 kayi sharing ma abokanka
musulmi zuwa wani group don mu amfana baki daya



 Matakai 5 da zaka Sauke Alqur'ani cikin watan Ramadan ⤵️


1= Yadda zaka sauke Alqur'ani a watan Ramadan { Cikin kwanaki 30} Ko wace rana Juz'i Daya:

* Asuba: Shafi 4
* Azahar: Shafi 4
* La'asar: Shafi 4
* Magriba: Shafi 4
* Isha'i: Shafi 4

2= Yadda zaka sauke Alqur'ani a watan Ramadan { Cikin kwanaki 15} Kawace Rana Juz'i 2:

* Asuba: Shafi 8
* Azahar: Shafi 8
* La'asar: Shafi 8
* Magriba: Shafi 8
* Isha'i: Shafi 8

3= Yadda zaka sauke Alqur'ani a watan Ramadan { Cikin kwanaki 12} Kawace Rana Juz'i Biyu da Rabi:

* Asuba: Shafi 10
* Azahar: Shafi 10
* La'asar: Shafi 10
* Magriba: Shafi 10
* Isha'i: Shafi 10

4= Yadda zaka sauke Alqur'ani a watan Ramadan { Cikin kwanaki 10} Kawace Rana Juz'i 3:

* Asuba: Shafi 12
* Azahar: Shafi 12
* La'asar: Shafi 12
* Magriba: Shafi 12
* Isha'i: Shafi 12

Wannan kuma Bangare ne na masu Himma ta gaske.

5= Yadda zaka sauke Alqur'ani a watan Ramadan { Cikin kwanaki 6} Kawace Rana Juz'i 5:

* Asuba: Shafi 20
* Azahar: Shafi 20
* La'asar: Shafi 20
* Magriba: Shafi 20
* Isha'i: Shafi 20

 Ku tayani Yada wannan Alkhairi domin bamu san adadin Ladan da Ni da Ku zamu samu ba yayinda wani ya sauke Alqur'ni ta dalilin karanta wannan Jawabi ba.

📝Rubutawa: Dan Uwanku a Musulunci: Muhammad Lawan Bin Musa { Abu- Ja'afar }.





Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

DailyAdhkar


#DailyAdhkar

• Laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa Huwa 'alaa kulli shay'in qadeer — either 100 times or 10 times or 1 time

The Prophet Muhammad (ﷺ) said: "Whoever says:

« لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهْوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ‏ »

(None has the right to be worshipped except Allah, alone, without any partner, to Him belong all sovereignty and praise, and He is over all things omnipotent)

one hundred times will get the same reward as given for freeing ten slaves; and one hundred good deeds will be written in his accounts, and one hundred sins will be deducted from his accounts, and it (his saying) will be a shield for him from Satan on that day till night, and nobody will be able to do a better deed except the one who does more than he."

📚: Sahih Bukhari 6403

The Prophet Muhammad (ﷺ) said: "He who uttered:

« لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهْوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ‏ »

ten times, he is like one who freed four slaves from the progeny of Ismail."

📚: Sahih Muslim 2693 (6844)

The Prophet Muhammad (ﷺ) said: "Whoever says:

« لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهْوَ عَلَى كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ‏ »

in the morning will have a reward equivalent to that for setting free a slave from among the descendants of Isma'il. He will have ten good deeds recorded for him, ten evil deeds deducted from him, he will be advanced ten degrees, and will be guarded from the satan till the evening. If he says them in the evening, he will have a similar recompense till the morning."

📚: Sunan Abi Dawud 5077 | Sahih






Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...