Thursday, 14 April 2022

{{NASIHAR RANAR JUMMA'A}} (Hijirah 08-08- 1443)


Yau zamuja hankulan yan uwana musulmi kan lura da ayoyin Allah subahanahu wata'ala,,.  Dan uwa kasani cewa baka zama cikin mummunai inbaka tunani da lura kan ayoyin Allah,  yar uwa kisan dahaka,,

Meye anfanin zuciyar ka dan uwana da baka tuna Allah da ita, ta lura da ayoyin shi abankasa?  Meye anfanin zuciyar ki yar uwa dabakya tuna Allah da ita?   Meyesa bazakyi tunani ba,  

Kazauna kayi tunani dan uwana kaduba saman nan ya'akayi akaginata, kaduba kasan nan ya'akayi aka shimfidata, ka duba duwatsu da tekunan kaduba canjin dare da rana, kullun sai anyi dare kullun sai anyi rana toh dare da ranan nan suna zuwa kafin kai kuma zaka bar su, lalle yakamata kasan Allah inde kanada hankali, inde kina da lafiyayyen tunani yar uwata,,

Lura da dare da rana da jujjuya al'amura Allah yace ayace ga masu hankali, kai baka cikin masu hankalin ne,? Ke bakya ciki ne yar uwa?  Toh meye yasa bakwa tunawa,,. ?  Toh siffar bayin Allah mummunai suna lura da tunani akan ayoyin Allah,    sbd Allah bai haliice su don ayi wasa ba,,.   Bai halicce su ba don kawai ashentake amore,  a a ya halicce sune don suzame mana aya mubauta mishi shi kadai,, 
Allah yace>>

{{إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لَآيَاتٍ لِّأُولِي الْأَلْبَابِ

Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.

191
الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللَّهَ قِيَامًا وَقُعُودًا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَٰذَا بَاطِلًا سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّار

Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: (suna cewa "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.}}

Toh yan uwa muke tunawa da lura da ayoyin Allah abankasa, domin samun tabbatuwar imani azukatan mu,,,  kar mudauki tunin turawa na  kawai Allah yakawomu duniyar nan don mushentake، muyi abunda mukaga dama,  duk ko wanda yabiyewa tunanin su, toh baizaiyi kishin Allah ba  , bazaiyi kishin Annabi s.a.w ba bazaiyi kishin Addinin musulunci da musulmai ba,,  saboda sun lalata mishi tunanin shi,,. Allah yarufamana asiri,,

Yaa Allah kasamu cikin bayinka masu tunawa da lura da Ayoyin ka, yaa ka gafarta mana mu da iyayenmu Baki daya,,yaa Allah ka albarka ci rayuwar mu, yaa Allah ka dauramu kan hanya madedeciya, ameen,




Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...