ALƘUR'ÃNI DA AZUMI SUNA YIN CETO.
-
"A ranar ƙiyamah alƙur'ani da azumi za suyi ceto ga bayi waɗanda suka kasance ma'abotansu ne a wannan duniyar, waɗanda suka ƙarar da rayuwarsu wajen yin ta'ammuli dasu a duniya"
-
"Kowane daga cikinsu zai nemi Allah ta'ala ya bashi ceton dukkanin bawan da ya kasance yana neman kusanci da Allah dominsu, sai Allah buwayi ya basu ceton waɗannan bayin nan-take"
-
"Ruwaya daga Abdullahi ɗan Amru, lallai Manzon Allah ﷺ, yace: azumi da alƙur'ani suna yin ceto ga bawa a ranar ƙiyamah, azumi zai ce: haƙiƙa ya ubangiji, ni na hanashi abinci, da sha'awa da rana, to ka bani ceton sa. alƙur'ani kuma sai yace: haƙiƙa na hanashi yin bacci da daddare, to ka bani ceton sa, sai yace: sai suyi ceton"
Ahmad ne ya ruwaito
No comments:
Post a Comment