Sunday, 17 April 2022

ASÃRA MAFI GIRMA AWA

ASÃRA MAFI GIRMA AWATAN RAMADÃN
══════ ❁✿❁  ═══════
TA FARKO.
Kai Baka Tsaya Anyi Sallar-Tarãwĩhi da Kai ba, Kuma Kai Baka Tãshi Cikin Dare Kãyi Wata Ibdah ba, Sa'annan daga Cin Abincin Sahur, Ka Koma Bacci  Baka Sãmu Sallar-Asubahi ba.
LALLAI KA TAFKA ASÃRA
══════ ❁✿❁  ═══════
TA BIYU.
Ramadãn Na Neman Tafiya, Amma Har Yanzu Baka Sauke (ALQUR'ÃNI) Koda Sau ɗaya ba, Gãshi Kai Bãbu Ruwanka da Zuwu Jin Tafsĩri, Kã Kãsa Zuwa Kõda Na Yini ɗaya, Kuma 'Yar Sadakar Nan da Ake Kaiwa Masallaci Don Taimakon Marãyu, Ko Dabĩno da Ruwan Sanyi da Ake Kaiwa Don Sãmun Lãdan Masu Azumi, Babu Kai Aciki.
WANNAN BA 'KARAMAR ASÃRA BANE
══════ ❁✿❁  ═══════
TA UKU.
Ana Azumi Amma Kai Babu Ruwanka da Ambaton Allah, Sai Buga Game a Handset da Kallace-Kallencen Finãfinai da Gulmace-gulmace, da Musun-banza, Kuma alla-alla Kake yi Asha Ruwa Ka Kēta Alfarmar Daren Ramadãn da Sãbon Allah.
HM, ANYA KUWA!!!?
══════ ❁✿❁  ═══════
TA HU'DU.
Asãra Mafi Girma da Zaka  Tafka Shi Ne: A Sãmu Daren (Lailatul-Qadr) Yazo Ya Wuce Kana Shirga Bacci, Ko Kana  (Night-Browsing) Wanda Meyuwu wa, Wannnan Azumin Shĩne: Na 'Karshe A Rãyuwar ka Baka Sani ba.
ALLAH YA KYAUTA
══════ ❁✿❁  ═══════
#NASIHA
Kana da Sauran Lokacin da Zaka Rĩbata, Kwana (14) Ko (15) Suka Rage Maka, Wanda Acikin Su Ne (Lailatul-Qadr) Yake, Kada Kace Sai A Goman 'Karshe Zaka Neme Shi, A'ah, Ka Fara Rãya Dararen da Suka Rage Tun daga Yau Har Zuwa 'Karshen Ramadãn dan Sãmun Tabbacin Muwãfaqa da Lailatul-Qadr.
══════ ❁✿❁  ═══════
FÃTAN ALKHAIRI.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TAMBASIRUNIGERIALIMITED

MUTANE (7) ƳAN ALJANNAH 

Manzon Allah ﷺ, yace: *"mutane bakwai Allah yana inuwantar dasu a cikin inuwarsa a ranar da babu wata inuwa face sai inuwarsa"*
📒 Sahih Al-Bukhari (660)

👉🏿 *Shugaba mai adalci*, (shine wanda yake tabbatar da adalci a cikin talakawansa).

👉🏿 *Da matashi wanda ya rayu cikin bautar ubangijinsa (Allah).*

👉🏿 *Da mutumin da zuciyarsa ta ratayu (ta ƙullu ko ta shaƙu) da masallaci.*

👉🏿 *Da mutane biyun da suke soyayya domin Allah, suka haɗu dominsa, kuma suka rabu dominsa.*

👉🏿 *Da mutumin da mace ma'abociyar nasaba da kyawu ta nemeshi*, sai yace, *ni ina jin tsoron Allah.*

👉🏿 *Da mutumin da yayi sadaƙa, ya ɓoyeta*, hagunsa bata san me damansa ta bayar ba.

👉🏿 *Da mutumin da ya tuna Allah shi kaɗai, sai idaniyarsa ta zubar da ƙwalla, (hawaye).*
📒 Sahih Al-Bukhari (660)

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇https://t.me/TAMBASIRUNIGERIALIMITED








Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...