A SAURARI WANNAN VIDIO DOMIN JIN CIKAKKEN BAYANI DAGA BAKIN SHEIKH IBARAHIM MANSUR KADUNA NIGERIA R, T, A
Friday, 8 April 2022
001 CIGABAN TARIHIN ANNABI MUHAMMADU S A W SADAUKAN TAKAR SA JARUMI NE ...
001 CIGABAN TARIHIN ANNABI MUHAMMADU S A W SADAUKAN TAKAR SA JARUMI NE KARFIN KUDURA NE DASHI SAW
Thursday, 7 April 2022
FALALAR YIN SALLAR ASHAM
___________
Ankarbo daga sayyadi Aliyu dan Abi Dalib
(RTA) yace
Na tambayi manzon Allah (SAW) acikin Falalar
yin sallar Asham Acikin wata Ramadan sai
Manzon Allah (SAW) yace
▓•Wanda yayi Asham adare na farko Awatan
Ramadan mumini yana fita daga cikin laifinsa
kamar yadda mahaifiyarsa ta haifeshi,
▓•Wanda yayi Asham Adarena 2 Allah zai
gafartawa iyayansa,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 3 Wani Mala'ika zaikira sunansa a karkashin Al'arshi yace
Anunka aiyukan Alkhairi kuma agafarta
laifukansa,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 4 za'a bashi ladan wanda yakaranta Attaura, Injila, zabura,
da Alqur'ani,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 5 Za'a bashi ladan yayi
sallah a makka da Madina,
▓•Wanda yayi Asham Adare na 6 za'a bashi
ladan mala'ikun da suke kewaye da Baitul
ma'amuri kuma dukkan dutse da marmara
zasu nemi agafarta masa laifukansa
▓•Wanda yayi Asham Adare na 7 kamar yariski
Annabi musa ne yataimakeshi akashe Fir'auna
da Hamana,
▓•Wanda yayi adare na 8 Allah zaibashi ladan
daya bawa Annabi Ibrahim,
▓•Wanda yayi adare na 9 Kamar ya bautawa Allah ne irin wadda Annabi Muhd (SAW)
Yayiwa Allah,
▓•Wanda yayi adare na 10 Allah zai'azurtashi Da
Alkhairan duniya da lahira,
Wanda yayi adare na 11 zai fita daga duniya
kamar yadda aka haifeshi,
▓•Wanda yayi adare na 12 zaizo ranar Alkiya
yana Amintacce
▓•Wanda yayi adare na 13 Allah zaigina masa
birni Agidan Aljanna,
▓•Wanda yayi adare na 14 Mala'iku zasuzo suyi
masa shaidar yayi sallar Asham baza aimasa hisabiba,
▓•Wanda yayi adare na 15 Mala'iku zasuyi masa
salati da madauka Al'arshi da kursiyu
▓•Wanda yayi adare na 16 Allah zai rubuta
sunansa daga masu kubuta daga wuta,
▓•Wanda yayi adare na 17 za'a bashi lada kamarna dukkan Annabawa,
▓•Wanda yayi adare na 18 wani mala'ika zai
kiransa yace yakai bawan Allah
Allah ya yarda dakai da mahaifanka
▓•Wanda yayi adare na 19 Allah zaidaga
matsayinsa a Aljanna Firdausi,
Ya Allah kabamu rabo duniya da lahira
ءمب
Kuyi Sherin Dan Karuwar Yan Uwa Musulmai
Wednesday, 6 April 2022
KADA KA BAR HARSHENKA YA BUSHE DAGA AMBATON ALLAH (ﷻ)
🇭 🇦 🇩 🇮 🇹 🇭:
KADA KA BAR HARSHENKA YA BUSHE DAGA AMBATON ALLAH (ﷻ)
Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:
عن عبد الله بن بسر رضي الله عنه، قال (لما شكا الرجل حاله قال: يا رسول الله! إن شعائر الإسلام قد كثرت عليَّ فأخبرني بأمر أتشبَّثُ به، قال: (لا يزال لسانك رطباً من ذكر الله)
[رواه الترمذي وصححه الألباني]
An Karɓo Daga Abdallahi bn Basr (ra), Yace: Yayin Da Wani Mutum Yazo da Ƙorafi Yace: Ya Manzon Allah (ﷺ)! Lallai Ayyukan Musulunci Sunyi Yawa Agareni, Ka Sanar Dani Wani Abinda Zanyi Riƙo Dashi. Sai Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Kada Harshenka Ya Gushe A Jiƙe Daga Ambaton Allah”.
(Tirmizi Ya Ruwaitoshi, Kuma Albani Ya Ingantashi)
Yana daga Cikin Falalar Ambaton Allah, Shine Yanda Manzon Allah (ﷺ) Ya Fifita Ambaton Allah Sama da Duk Abinda Ke Cikin Duniyar Nan.
عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((لأن أقول سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله، والله أكبر أحبُّ إليَّ ممَّا طلعت عليه الشمس))
(رواه مسلم)
An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Na Faɗi SUBHANALLAH, WAL HAMDULILLAH, WA LA'ILAHA ILALLLAH, WALLAHU AKBAR, Yafi Soyuwa Gareni Sama da Duk Abinda Rana Ta Fito Akansa”.
(Muslim Ya Ruwaitoshi)
Yana Daga Cikin Fa'idar Zikiri, Yanda Ubangiji (ﷻ) Yayi Alƙawarin Ambaton Wanda Ya Ambaceshi. Wannan Falalar Kaɗai Ta Ubangiji (ﷻ) Zai Tuna Wanda Ya Tunashi Ta Isa Tasa Duk Wani Musulmi Ya Hanu Daga Shagaltuwa Ga Barin Ambaton Allah (ﷻ).
Allah (ﷻ) Yana Cewa:
﴿ فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ ﴾
[البقرة: ١٥٢]
“Sabõda Haka, Idan Kuka Tuna Ni, Zan Tunã Ku, Kuma Ku Yi Gõdiya Gare Ni, Kuma Kada Ku Butulce Mini”.
(Baƙara: 152)
Sheikhul Islam Ahmad Bn Abdulhalim (rh) Yana Cewa:
(الذكر للقلب مثل الماء للسمك، فكيف يكون حال السمك إذا فارق الماء؟!)
“Ambaton Allah Ga Zuciya Kamar Ruwa Ne Ga Kifi. Yaya Halin Kifi Zai Kasance Idan Ya Rabu da Ruwa?!”
Ibn Aun (rh) Yana Cewa:
(ذكر الناس داء، وذكر الله دواء)
“Ambaton Mutane Cuta Ne, Ambaton Allah Kuma Magani Ne”.
Yahya bn Mu'az (rh) Yana Cewa:
(حادثوا القلوب بذكر الله تعالى، فإنها سريعة الغفلة، فاللسان لا بدَّ له أن يتكلم إما بخيرٍ أو بشـرٍّ أو بأمرٍ مباح، فانظر لنفسك ألا تتكلَّم إلا بما يرضي ربَّك عز وجل وتجده في صحيفتك يوم القيامة، ومن أعظم العقوبات الغفلة عن الذكر)
“Ku Zanta Da Zuciyoyi da Ambaton Allah Maɗaukaki, Domin Tanada Saurin Gafala. Babu Makawa Harshe Sai Yayi Magana; Kodai Zancen Alkhairi Ko Na Sharri Ko Kuma Abinda Yake Na Halas. Ka Dubi Kanka, Kada Kayi Magana Sai Da Abinda Allah Ya Yarda Dashi, Domin Zaka Samu Duk Abinda Ka Furta a Cikin Littafinka Ranar Alƙiyama. Yana Daga Cikin Mafi Girman Uquba, Shine Gafala Daga Ambaton Allah”.
Allah (ﷻ) Yana Cewa:
﴿وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَنْ ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ وَكَانَ أَمْرُهُ فُرُطًا﴾
[الكهف: ٢٨]
“Kuma Kada Kabi Wanda Muka Shagaltar Da Zũciyarsa Daga Ambaton Mu, Kuma Ya Bi Son Zuciyarsa, Alhãli Kuwa Al'amarinsa Ya Kasance Yin Ɓarna”.
(Kahfi: 28)
Daga Ƙarshe, Ubangiji (ﷻ) Yana Cewa:
(الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُمْ بِذِكْرِ اللَّه أَلا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ)
[سورة الرعد: ٢٨]
“Waɗanda Suka Yi Ĩmãni Kuma Zukãtansu Sukan Natsu Da Ambaton Allah. To, Da Ambaton Allah Zukãta Suke Natsuwa”.
(Ra'ad: 28)
YA ALLAH KA NATSAR DA ZUKATAN MU DA AMBATONKA, KA SANYA MU CIKIN BAYINKA DA ZAKA AMBATO CIKIN DANDAZON MALA'IKUNKA
✍🏽Abu Aysha Al-Maliky
🕌🇦 🇿 🇰 🇦 🇷
AZKAR OF THE DAY
➖➖➖➖➖➖➖➖
🌺 Recite this Azkar in the morning and evening 10 times and get lot of hasnah..
---------------------------------
Bismillahirrahmanirraheem
---------------------------------
🌷 ✦ La ilaha illAllah wahdahu la sharika lahu, lahul-mulk wa lahul-hamd Yuhi wa Yumeet, wa huwa Ala kulli shayin qadir
✦ *لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ*
✦There is no Lord except Allah , Alone with no partner, to Him belongs the dominion, and to Him is all the praise, He gives life and death, and He has power over all things
✦ : Abu Ayyub Ansari Radi Allahu Anhu narrated that: Rasool Allah Sallallahu Alaihi wasallam said: Whoever says these words ten times in the morning , for every one time Allah subhanahu will write 10 good deeds for him , Will wipe away 10 evil deeds and will raise 10 degrees for him, and these words will be equal for him as he has freed 10 captives ( if anybody say 10 times then this rewards will be ten fold) and it will be his weaopan from the beginning of the day untill the end of the day. and that day nobody will be able to do any deeds which is more better than this and if he say same words in the evening will get same rewards
Al-Silsila-tus-Sahiha-2967-Hasan
DARUSAN RAMADHAN
Darasi na Uku: Hukuncin Azumin Ramadhan
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya halicci bayi, kuma ya shar'anta musu hukunce – hukunce da suka dace da rayuwarsu, kuma ya yi tanadin sakamako ga wanda ya kiyaye dokokinsa, da kuma alkawarin narkon azaba ga wanda ya saba masa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Ya ku 'yan'uwana, lallai Azumin watan Ramadhan daya ne daga cikin rukunnan Muslunci da abubuwan da aka gina shi a kansu, Allah ya ce:
{Ya ku wadanda suka yi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, don ku samu tsoron Allah. Ranaku ne kirgaggu, duk wanda ya kasance maras lafiya daga cikinku ko yana halin tafiya to ya kirga a wasu ranakun daban…} [al-Baqara: 183 - 184].
Annabi (saw) ya ce: ((An gina Muslunci a kan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma Annabi Muhammad ma'aikin Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da Zakka, da aikin Hajji, da Azumin watan Ramadhan)). Sahihul Bukhari (8), Sahihu Muslim (16).
Musulmai sun yi Ijma'i a kan farlancin Azumin watan Ramadhan da kasancewarsa abu sananne wanda babu shakka a kansa a cikin Addinin Muslunci. Kuma sun yi Ijma'i yankakke babu shakka a cikinsa; duk wanda ya yi inkarin wajabcinsa to hakika ya kafirta, za a nemi ya tuba, idan ya tuba, ya yarda da wajabcin Azumin shi kenan, idan kuma ya ki tuba to za a kashe shi a matsayin kafiri, wanda ya yi ridda daga Muslunci. Ba za a yi masa wanka ba, ba za a suturce shi a likkafani ba, ba za a yi masa Sallah ba, ba za a yi masa addu'an neman rahma ba, ba za a bisne shi a makabartan Musulmai ba, kawai za a tona rami ne a can nesa a rufe shi, don kar warinsa ya dami mutane, 'yan'uwansa su cutu.
An farlanta Azumin Ramadhan ne a shekara ta biyu bayan Hijirah, don haka Manzon Allah (saw) ya yi Azumin Ramadhan na tsawon shekaru tara. Kuma farlantawan ya kasance ne a matakai guda biyu:
Na farko: an bayar da zabi tsakanin yin Azumin ko ciyarwa a madadin haka, duk da cewa; Azumin shi ya fi falala.
Mataki na biyu: wajabta Azumin Ramadhan din a kan kowa ba tare da zabi ba. Ya tabbata daga Salama dan Akwa'u (ra) ya ce: ((Lokacin da fadin Allah ya sauka: {Akwai fansan ciyar da miskini a kan wadanda za su iya yin Azumin}, sai ya kasance wanda ya ga dama sai ya sha ruwa ya biya fansa, har sai da Ayar da take bayanta ta sauka, sai ta soke ta)). Sahihul Bukhari (4507), Sahihu Muslim (1145).
Wato yana nufin fadin Allah: {Duk wanda ya halarci watan a cikinku to wajibi ne ya azumce shi. Duk wanda ya kasance maras lafiya ko yana halin tafiya to ya kirga Azumin a wasu ranakun daban}. [al-Baqarah (185)]. Sai Allah ya wajabta Azumin a kan kowa ba tare da zabi ba.
Azumin ba ya wajaba har sai an tabbatar da shigan watan Ramadhan, don haka ba a yin Azumin kafin shigan watan, saboda fadin Annabi (saw):
((Kar dayanku ya gabaci watan Ramadhan da Azumin rana daya ko biyu, sai dai idan mutum ya kasance yana yin wani Azumi na musamman to sai ya azumci ranar)). Bukhari (1914).
Ana yanke hukuncin shigan watan ne da dayan abubuwa guda biyu:
Na farko: ganin jinjirin watan Ramadhan. Allah ya ce:
{Duk wanda ya halarcin watan a cikinku to wajibi ne ya azumce shi}.
Da fadin Annabi (saw): ((Idan kun ga jinjirin watan to ku yi Azumi)). Bukhari (1907) Muslim (1080).
Ba a shardanta dole sai kowane mutum ya gani da kansa ba, a'a, idan mutumin da shaidarsa za ta tabbatar da shigan wata ya ga jinjirin watan shi kenan yin Azumin ya wajaba a kan kowa.
Amma sharadi ne wajen karban shaidar ganin watan sai mai ba da shaidar ya zama Musulmi baligi mai hankali, wanda ake yarda da maganarsa saboda yana da amana, kuma idonsa lafiya kalau yake. Amma kafiri ko yaro ko mahaukaci shigan wata ba ya tabbata da shaidarsu, saboda Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce: ((Wani bakauye ya zo wajen Annabi (saw) sai ya ce: Lallai na ga jinjirin wata (yana nufin watan Ramadhan), sai Annabi (saw) ya ce: "Shin ka shaida babu abin bauta bisa cancanta sai Allah?" Sai ya ce: Eh.
Ya ce: "Ka shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne?" Ya ce: Eh. Sai Annabi (saw) ya ce: "Bilal, ka sanar da mutane gobe su yi Azumi")). Abu Dawud (2340), Tirmiziy (691), Nasa'iy (2113), Ibnu Majah (1652).
Haka wanda aka san shi da karya, ko gaggawan ba da labari, ko mai raunin ido to shi ma ba a karban shaidarsa a ganin wata.
Kuma ko da mutum daya ne ya ba da shaidan ganin wata za a karba, saboda Hadisin Abdullahi dan Umar (ra) ya ce: ((Mutane sun nemi ganin jinjirin wata, sai na ba da labari wa Annabi (saw) cewa; na ganshi, sai ya dauki Azumin, kuma ya umurci mutane da su yi Azumin)). Abu Dawud (2342).
Duk wanda ya ga jinjirin wata bisa yakini to wajibi ne ya sanar da shugabannin hukuma, haka watan Shawwal ma. Saboda duk abin da sai da shi wajibi ya cika shi ma wajibi ne.
Amma idan mutum ya ganshi a wajen da yake ba zai iya sanar da shugabanni ba, to shi zai dauki Azumin, sai kuma ya yi iya kokarinsa wajen isar musu gwargwadon iyawarsa.
Idan shugabanni suka sanar da ganin wata a kafafen yada labarai to wajibi ne a yi aiki da sanarwar tasu, wajen shigan watan Ramadhan ko waninsa, saboda sanarwan hukuma hujja ne a Shari'a, ya wajaba a yi aiki da ita. Shi ya sa Annabi (saw) ya umurci Bilal da ya sanar da mutane ganin wata, bayan an tabbatar masa da ganin watan.
Kuma abin lura wajen shigan watan Ramadhan shi ne gani da ido ba lissafi ko amfani da ilimin taurari ba, kamar yadda Hadisai suka nuna cewa; da gani za a yi aiki.
Abu na biyu: ana yin hukunci da shigan watan Ramadhan da cikan watan Sha'aban kwana talatin, saboda wata ba ya wuce kwana talatin, kuma ba ya gaza kwana ishirin da tara. Don haka idan ba a samu tabbacin ganin wata a ranar ishirin da tara ba, imma saboda gajimare ko wani abin daban to sai a cika lissafin watan Sha'aban ya cika kwana talatin, bayan haka sai a yi hukunci da shigan watan Ramadhan. Annabi (saw) ya ce:
((Ku yi Azumi saboda ganin wata, ku sha ruwa (ranar Sallah) saboda ganinsa, amma idan an yi gajimare ya tare muku ganin watan to ku kirga (watan Sha'aban) ya cika kwana talatin)). Bukhari (1909), Muslim (1081).
Allah ya sa mu dace ga bin shiriya, ya ba mu albarkan da ke cikin wannan wata, ya taimake mu a kan yawaita ibada da aiyukan da'a a cikinsa, da nisantar saba masa. Allah ya ba mu tsaro da zaman lafiya a kasarmu, da sauran kasashen Musulmi gaba daya.
Dr. Aliyu Muh'd Sani
Ya ce: "Ka shaida Annabi Muhammadu
Ya ce: "Ka shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne?" Ya ce: Eh. Sai Annabi (saw) ya ce: "Bilal, ka sanar da mutane gobe su yi Azumi")). Abu Dawud (2340), Tirmiziy (691), Nasa'iy (2113), Ibnu Majah (1652).
Haka wanda aka san shi da karya, ko gaggawan ba da labari, ko mai raunin ido to shi ma ba a karban shaidarsa a ganin wata.
Kuma ko da mutum daya ne ya ba da shaidan ganin wata za a karba, saboda Hadisin Abdullahi dan Umar (ra) ya ce: ((Mutane sun nemi ganin jinjirin wata, sai na ba da labari wa Annabi (saw) cewa; na ganshi, sai ya dauki Azumin, kuma ya umurci mutane da su yi Azumin)). Abu Dawud (2342).
Duk wanda ya ga jinjirin wata bisa yakini to wajibi ne ya sanar da shugabannin hukuma, haka watan Shawwal ma. Saboda duk abin da sai da shi wajibi ya cika shi ma wajibi ne.
Amma idan mutum ya ganshi a wajen da yake ba zai iya sanar da shugabanni ba, to shi zai dauki Azumin, sai kuma ya yi iya kokarinsa wajen isar musu gwargwadon iyawarsa.
Idan shugabanni suka sanar da ganin wata a kafafen yada labarai to wajibi ne a yi aiki da sanarwar tasu, wajen shigan watan Ramadhan ko waninsa, saboda sanarwan hukuma hujja ne a Shari'a, ya wajaba a yi aiki da ita. Shi ya sa Annabi (saw) ya umurci Bilal da ya sanar da mutane ganin wata, bayan an tabbatar masa da ganin watan.
Kuma abin lura wajen shigan watan Ramadhan shi ne gani da ido ba lissafi ko amfani da ilimin taurari ba, kamar yadda Hadisai suka nuna cewa; da gani za a yi aiki.
Abu na biyu: ana yin hukunci da shigan watan Ramadhan da cikan watan Sha'aban kwana talatin, saboda wata ba ya wuce kwana talatin, kuma ba ya gaza kwana ishirin da tara. Don haka idan ba a samu tabbacin ganin wata a ranar ishirin da tara ba, imma saboda gajimare ko wani abin daban to sai a cika lissafin watan Sha'aban ya cika kwana talatin, bayan haka sai a yi hukunci da shigan watan Ramadhan. Annabi (saw) ya ce:
((Ku yi Azumi saboda ganin wata, ku sha ruwa (ranar Sallah) saboda ganinsa, amma idan an yi gajimare ya tare muku ganin watan to ku kirga (watan Sha'aban) ya cika kwana talatin)). Bukhari (1909), Muslim (1081).
Allah ya sa mu dace ga bin shiriya, ya ba mu albarkan da ke cikin wannan wata, ya taimake mu a kan yawaita ibada da aiyukan da'a a cikinsa, da nisantar saba masa. Allah ya ba mu tsaro da zaman lafiya a kasarmu, da sauran kasashen Musulmi gaba daya.
Dr. Aliyu Muh'd Sani
Tuesday, 5 April 2022
*LOKUTAN_AMSAR _ADDU'A*
Don Allah ko bazaka karanta ba katura a groups saboda Al'umma su Amfanq da kai
Kowanne lokaci idan mutum yayi addu'a Allah yana karba.
Sai dai Ubangiji cikin baiwarsa
da falalarsa ya ke'banci wasu
lokuta ya sanya musu albarka
da baiwa fiye da sauran lokutai..
Wadannan lokutan sun hada da:
1. DAREN JUMA'A: Wato ranar
alhamis da dare, da kuma
wunin jumu'ar. Ma'aikin Allah
(alaihis salam) yace "babu wani
bawa wanda zai dace yana addu'a acikinta fache sai Allah
ya amsa masa".
2. WATAN RAMADHAN: gaba
dayansa lokaci ne na amsar
addu'a.
3. LAILATUL QADARI: Shima
lokacin amsar addu'a ne.
4. TSAKAR DARE: Musamman ma sulusin karshensa.. Lokaci ne da Allah yake gwanjon rahamarsa ga bayinsa.
5. LOKACIN DA AKE KIRAN
SALLAH, DA KUMA TSAKANIN
KIRAN SALLAH DA TADA IQAMAH.
6. LOKACIN DA AKA IDAR DA
SALLOLIN FARILLAH.
7. LOKACIN DA AKA GAMA
KARATUN ALQUR'ANI, KO
WA'AZI KO WATA KOYARWA TA
ILMI: Shima lokacin karbar addu'a ne.
8. LOKACIN DA ZAKARA YAYI CHARA. Shima lokacin amsar
addu'a ne.
9. LOKACIN TAFIYA TA ALHERI:
kamar tafiya hajji, sada zumunci, jihadi, ko fatauci.
Shima lokacin amsar addu'a.
10. RANAR ARFA: awannan
ranar, da wanda yake Makkah,
da wanda yake gida, duk Allah
yana amsar addu'arsu.
11. LOKACIN ZUBAN RUWAN
SAMA_ Shima ana amsar addu'a acikinsa.
12. LOKACIN DA AKA TSAIDA
SAHUN YAQIN DAUKAKA
KALMAR ALLAH.. Shima ana
amsar addu'a cikinsa.
13. LOKACIN DA MUTUM YAYI
SUJJADAH. Shima ana amsar
addu'a cikinsa.
14. LOKACIN DA MUTUM YA
FARKA DAGA BARCI: musamman idan mutum ya karanta "sub'hanallah wal'hamdulillah, wa la'ilaha'illal-Lah wallahu akbar" (QAFA 10). Duk abinda ka roka Mustajabah.
Don Allah duk wanda yakaranta yatura a groups 3 tunatarwa ga wanda basuyi like ɗin wannan page suyi like ko following Sabiida faɗakarwa na gaba
ALLAH YA SA MU DACE.. Allah ya
sakawa Malam Da Alheri
Saturday, 2 April 2022
TASKAR ILLIMANTARWA:
Mal. Aminu Ibrahim Daurawa.:
SHIGA WATAN RAMADAN
ANA SHIGA WATAN RAMADAN NE TA HANYOYI GUDA BIYU, BABU TA UKU.
Hanya ta farko: ganin jinjirin wata, shi ganin wata zai iya kasancewa ta fuskoki guda huɗu:
Mutum ɗaya tak ya ga wata shi kadai , wato babu wanda ya gani a duk garin sai shi kadai.
Mutum biyu su gani su kadai a garin gabaɗaya, in banda su babu wanda ya gani.
Mutane da yawa su ga wata a gari ɗaya, sauran garuruwa kuma ba a gani ba. Misali, kamar mutan gari ɗaya, ko unguwa ɗaya, ko layi ɗaya, ko yanki ɗaya, ya zamo su kadai ne suka ga wata.
A ga wata a guraruwa daban-daban a waje daban-daban ko a qasashe daban-daban.
Waɗannan su ne matakan da ake ganin wata ta qarqashinsu.
Idan aka tabbatar da ganin wata ta ɗayan waɗannan matakai, shugabanni suka amince da ganin ta hanyar bin diddigi, sai a ba da sanarwar kowa ya ɗauki azumi.
Hanya ta biyu: Idan ba a ga wata ba, wato babu wanda ya ga wata a gari, ko unguwa, ko qasa, mutum ɗaya ko biyu ko jama'a da yawa, ko kuma an sami wanda ya gani sai dai ba a yarda da ganin nasa ba. Sai a cika lissafin Sha’aban ya zamo kwana talatin (30) daidai.
Ita wannan hanyar ba sai an tsaya neman wanda ya ga wata ba, tun da watan Sha’aban ya cika kwana talatin (30), don haka washegari sai kowa ya tashi da azumi ba sai ya jira umarnin shugaba ba.
Don haka waɗannan su ne hanyoyin da ake shiga watan Ramadan ta cikinsu.
Hujjojin da suka tabbatar da hakan su ne:
Ta farko: hadisin Abdullahi Ɗan Umar رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ambaci watan Ramadan sai ya ce, “Shi dai wata kwana ashirin da tara (29) ne.”
A wata ruwayar ya ce, “Shi wata haka ne, da haka, da haka.” sai ya haɗa 'yan yatsunsa na dama da hagu, wato yana nufin goma da goma sau biyu ashirin (20) kenan, goma ta uku kuma sai ya lanƙwashe ɗan yatsansa guda ɗaya tara kenan. A wata ruwayar kuma yana cewa, “Shi wata wani lokaci yana yin talatin (30) wani lokaci kuma yana yin ashirin da tara (29), don haka kada ku yi azumi sai kun ga wata, kada ku ajiye sai kun gan shi, idan aka yi muku lullumi, sai ku cika lissafin Sha’aban ya zama talatin (30).” ()
A ruwayar Ummu Salamah kuwa cewa ta yi, Manzon Allah ﷺ ya yi rantsuwa ba zai je wajen iyalinsa ba sai bayan wata guda, to yayin da kwana ashirin da tara (29) suka wuce, sai ya yi sammako ya shiga wajen iyalinsa da daddare, sai wadda ya shiga wajenta ta ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ, ai ka rantse cewa ba za ka shiga wajen matanka ba, har tsawon wata guda, ya aka yi kuma ka shigo yanzu? sai ya ce, "Lallai shi wata yakan yi kwana ashirin da tara (29) ne." ()
Shi kuma hadisin Abu Bakarata رضي الله عنه da ya ruwaito daga Ma’aiki ﷺ yana cewa, “Watan Ramadan da watan zulhajji ba sa tauyewa.” ()
Abin da Malamai suka fada a kan ma’anarsa shi ne: Ishaƙ Bn Rahawaihi da Ibn Suwaidin Bn Hubairah sun ce, ma'anar ba sa tauyewa shi ne ba a tauyewa mutum ladan ayyukan da ya aikata a cikinsu ko da kuwa sun tauye a lissafi, ba za su tauye a wajen ba da ladan aiki ba.
Shi kuma Muhammad Bn Sirina ya ce, ba za su haɗu a Shekara kowanensu ya tauye ba.
Shi kuma Imamu Ahmad yana cewa, idan Ramadan ya tauye to Zulhajji zai cika, idan kuma Zulhajji ya tauye to Ramadan zai cika.
Malam Alqasim Bn Muhammad ya ce, na ji Bazzaru yana cewa, waɗannan watanni biyu ba sa tauyewa a Shekara ɗaya a tare.
An ruwaito daga Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku yi azumi in kun ga wata, ku sauke in kun gan shi, idan hazo ko hadari ya rufe muku shi, ku cika kwana talatin (30) na Sha’aban.”
A wata ruwayar ta Muslim ya ce, “In kun ga wata ku yi azumi idan kun gani ku aje, idan girjije ko hadari ya tsare ku, sai ku cika lissafin Sha’aban.”
A wata ruwayar ta Muslim ya ce, “Ku yi azumi don ganin wata, ku ajiye don ganin wata, idan hazo ya rufe muku shi, sai ku qirga talatin (30).” ()
Haka nan hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ yana cewa, “Kada ku gabaci wata da yin azumin kwana ɗaya ko biyu, sai dai idan akwai wani azumi da mutum ya saba yi, (sai ya dace da waɗannan ranakun) babu laifi ya yi abinsa, shi asalin wata kwana ashirin da tara ne (29).” Wannan
lafazin Abu Dawud ne.
A taqaice za mu iya cewa hanyoyin ɗaukar azumi guda huɗu ne, kamar yadda muka gabatar.
Na farko shi ne, ganin mutum ɗaya adali, idan hukuma ta gamsu ya zama wajibi ga duk Musulmin da yake wannan garin ya ɗauki wannan azumin.
Dalili hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه inda yake cewa, wani mazaunin qauye ya zo wajen Manzon Allah ﷺ ya ce na ga wata, sai Annabi ﷺ ya ce da shi, “Ka shaida Allah ﷻ shi kaɗai ne ba shi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu ﷺ Manzon Allah ﷻ ne? Sai mutumin ya ce eh, sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ya kai Bilalu je ka ka yi shela ka sanar da mutane cewa su ɗauki azumi gobe.” () Sai dai hadisin yana da rauni, amma malamai sun yi aiki da shi.
Abin nufi yawancin malamai da shi suke aiki cewa za a karɓi shaidar mutum ɗaya adali a gari gabaɗaya.
Wannan shi ne ra'ayin Abdullahi Bn Mubarak, Imamus Shafi'i, da Imamu Ahmad, da Imamu Abu Hanifa, da malaman Kufa, kuma shi ne ra'ayin Jamhuru, sun qArfafi wannan da hadisin Abdullahi Ɗan Umar رضي الله عنه wanda yake cewa, mutane sun duqufa suna duban wata sai Allah ﷻ ya nuna min shi, sai na shaidawa Ma’aiki ﷺ cewa ni na ga wata, sai Ma’aiki Allahi ﷺ ya tashi da azumi kuma ya umarci mutane suka ɗauki azumin.” ()
Sai dai malam Ishak Bn Rahawaihi shi yana ganin ba za a ɗauki azumi da ganin mutum ɗaya ba, sai dai mutum biyu.
Wannan kuma shi ne ra'ayin Imamuna Malik, da Laisu Bn Sa’ad, da Sufyanussauri, da Abdurrahman Al-Auza'i.
Allah ya karɓi ibadar mu.
* * * *
Friday, 1 April 2022
SALLOLIN DARAREN WATAN RAMADAN
SALLOLIN DARAREN WATAN RAMADAN
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM. WA SALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALI MUHAMMADIN
.
1• Dare na Farko: Raka'a hudu Fatiha
da Qulhuwa Goma Sha biyar {15}
Kowace Raka'a.
.
2• Dare na Biyu: Raka'a hudu Fatiha
da Inna-Anzalnahu {20} Kowace
Raka'a.
.
3• Dare na Uku: Raka'a {10} Fatiha da
Qulhuwa {50} Kowace Raka'a.
.
4• Dare na Hudu: Raka'a {8} Fatiha da
Inna-Anzalnahu {20} Kowace Raka'a.
.
5• Dare na Biyar: Raka'a {2} Fatiha da
Qulhuwa {50} Kowace Raka'a. bayan Sallama, Allahumma Salli Ala
Muhammadin Wa Ali Muhammadin
{100}.
.
6• Dare na Shida: Raka'a {4} Fatiha da
Tabara Kowace Raka'a.
.
7• Dare na Bakwai: Raka'a {4} Fatiha da Inna-Anzalnahu {13} Kowace
Raka'a.
.
8• Dare na Takwas: Raka'a {2} Fatiha
da Qulhuwa {10} Kowace Raka'a,
Bayan Sallama Subahanallahi {100}
.
9• Dare na Tara: Raka'a {6} Tsakanin Magriba da Isha'i, Fatiha da Kursiyyu
{7} Kowace Raka'a. Bayan Sallama
Salati {50}
.
10• Dare na Goma: Raka'a {20} Fatiha
da Qulhuwa {30}
.
11• Dare na Sha daya: Raka'a {2} Fatiha da Inna'a-adayna Kalkausar
{20}.
.
12• Dare na sha biyu: Raka'a {8}
fatiha da inna-anzalnahu {30}
Kowace Raka'a.
.
13• Dare na sha Uku: Raka'a {4} Fatiha da Qulhuwa {25} Kowace
Raka'a.
.
14• Dare na sha Hudu: Raka'a {6}
Fatiha da Izazul {30} Kowace Raka'a.
.
15• Dare na Sha biyar: Raka'a {4}
Fatiha da Qulhuwa {100} Kowace Raka'a.
.
16• Dare na sha shida: Raka'a {12}
Fatiha da Alhakumu{12} kowace
Raka'a.
.
17• Dare na sha bakwai: Raka'a {2}
Fatiha da Surar data samu, A Raka'a ta farko Fatiha da Qulhuwa {100}
Bayan Sallama La'ilaha Illallahu{100}.
.
18• Dare na sha Takwas: Raka'a {4}
Fatiha da Inna A'adayna {50} Kowace
Raka'a.
.
19• Dare na sha Tara: Raka'a {50} Fatiha da Izazul kowace Raka'a.
.
20• Dare na 20, 21, 22, 23, da 24: A
cikin kowane dare daga wadannan
dararen za'ayi sallah Raka'a {8} da
abin da ya samu na daga karatu.
.
21• Dare na Ashirin da biyar: Raka'a {8} Fatiha da Qulhuwa {10} Kowace
Raka'a.
.
22• Dare na Ashirin da Shida: Raka'a
{8} Fatiha da Qulhuwa {10} Kowace
Raka'a.
.
23• Dare na Ashirin da Bakwai: Raka'a {4} Fatiha da Tabara, idan ba
zaka iya ba to da Qulhuwa {25}
Kowace Raka'a.
.
24• Dare na Ashirin da Takwas:
Raka'a {6} Fatiha da Kursiyyu {10} da
Qulhuwa {10} da Kawthar {10}. Bayan Sallama Salati {10}. Sallar dare
na Ashirin takwas a bisa aka same ta
a hadisai, Raka'a {6} fatiha da
Kursiyyu {10} da Qulhuwa {10} da
Kawthar {10}. Bayan Sallama Salati
{100}
.
25• Dare na Ashirin da Tara: Raka'a
{2} Fatiha da Qulhuwa {20} Kowace
Raka'a.
.
26• Dare na Talatin: Raka'a {12}
Fatiha da Qulhuwa {20} Kowace
Raka'a {8} Bayan Sallama Salati {100}.
Yana daga cikin ayyukan dararen Watan Ramadan Yin Salla Raka'a 1000. Yadda ake yi shi ne: za ka sallaci raka'a 20 a cikin dararen ashirin na watan (wato Goman farko da Goman ta biyu). Kana mai yin raka'a takwas bayan sallar magriba
kafin sallar isha'i, sannan raka'a 12 bayan sallar isha'i. Sannan a kwanakin goman karshe za ka rika yin sallah raka'a 30, raka'a takwas bayan magariba kamar ta farko, sannan raka'a 22 bayan isha'i. idan ka lissafa zaka ga kana da 700 a cikin watan gaba daya don haka saura raka'a 300, su kuma za ka yi su ne a darare na 19 da dare na 23. Wadannan salloli za ka yi raka'a dari-dari na wannan darare ba su shafi talatin din da za ka yi a dararen ba (wato ba za ka ce tunda sallar daya ce ba, kuma na yi talatin to sai na kawo saba'in sun zama dari ke nan. A'a ba haka ba ne, za ka sallaci wadannan ashirin din na daren 19, sannan ka kawo dari. Haka ma dare na 21 da na 23 za ka yi talatin-talatin dinsu kamar yadda aka zayyana a dararen goman karshe, sannan ka kawo dari-dari ka kara.
.
GA LISSAFIN YADDA YAKE:
.
1● Darare Ashirin na farko da raka'a
20×dare 20 = raka'a 400
.
2● Raka'a 30 × dare 10 = raka'a 300
sai ka tara su 400 + 300 = 700
.
3● Raka'a 100 × 3 ) dora 19, 24, 23)
= Raka'a 300, Saika tara da 700 Zai ba ka = 700 + 300 = 1000.
.
IDAN KUMA KA CE DORAWA ZA KA YI, TO LISSAFIN ZAI ZAMA
.
1● Darare 20 din farko kana da
raka'a 400
.
2● Darare 10 karshe kana da raka'a
300
.
3● Dararen 19, 21, 23 kana da 210
(wato idan ya zama ka dora. ne ba ka yi kowacce daban ba)
.
4● Don haka duka sun zama 400 +
300 + 210 = 910 ka ga ba su cika ba.
.
Allah Ya sa Mu Amfana Ilaheeey.
.......copied
Tasirai malam tv
AL falaki tv
Ramli da hisabi tv
Mafarkinka sirrinka tv
Gudun duniya tv
Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳
taskaasirai@gmail.com
08124763287
08144698283
Subscribe to:
Posts (Atom)
Domin samun mustajaba a kwana 9
Khatimin Allahu Muhammadu idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau 92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...

-
SIRRIN MALLAKAR MUTUM MACE KO NAMIJI Amman ajitsoron Allah kada kayishi don cuta ko San zuciya ga asirigaskiyane to ga asirin kamar haka ida...