Shin da gaske an fara Transaction da Pi ?
_________
https://minepi.com/Othman4340
Mutane da yawa sunyi ta bayyana Screenshot da hotunan yadda suka fara cinikayya da Pi Coin dinsu bayan sunyi KYC, wasu sunyi Odar wayoyi, wasu motoci da sauran su, shin wannan cinikayyar ko transaction din dai dai ne?
Amsa a takaice itace ba dai dai bane, wannan transaction din ba na gaskiya bane, na 'yan 419 ne, saboda dalilai kamar haka:
Idan muka koma kan "White Paper" din Pi Network wanda Dr. Nickolas Kakkolis suka rubuta dashi da abokan aikin sa a Pi, wato (Pi Core Team) za muga wajen da suka rubuta dogon bayani akan wasu abubuwa na ilimin Computer na Na'urori ko Software da ake kira "API" da "SDK", menene API da SDK?
"API" yana nufin "Application Programming Interface", kamar tsare-tsare ne da hanyoyi tare da kayan aikin Na'ura Mai kwakwalwa (Computer) wajen gina Computer Software, tare tsaftace duk wata matsala akan Software din, kafin da bayan anyi, wato dai "is a set of protocols and tools for building application software".
"SDK" kuma yana nufin "Software Development Kit", wato taron Software ne domin Gina Applications, package, software framework da sauran su akan Internet da Computer.
Kusan suna kama da API, wasu ma suna cewa duk daya ne, but in a real sense ba daya bane.
Wadannan abubuwan API da SDK sune Key, ko Mabudi da Makullin da su Dr. Nickolas suke rike dasu domin tantance duk wani Application na 'yan kasuwa, wadanda suka yarda zasu zuba Hajar su, kayayyakin su a kasuwar Pi ta hanyar amfani da Pi Browser har zuwa cikin wuraren hada hadar, wanda zai zo nan gaba.
Idan ka fahimci wannan bayanin toh sai muce maka:
Har yanzu Pi Network (su Dr. Nickolas) basu fitar da ko Application kwaya daya na wani kamfani da suka yarda a sayi kaya a hannun su ba, don haka duk wani kamfani daka gani cewa suna sayar da kaya Kuma suna karban Pi toh na karya ne, Pi Network basu san dasu ba.
Kuma zaka ga ba takan Pi Browser ake yin wancan hada-hadar ba, takan Chrome ne, ko Opera ko wani Application.
Yanzu haka ana cewa akwai kamfanoni da Applications da kungiyoyi daban daban fiye da dubu 13,000 daga sassa daban daban na duniya wadanda suka aike da Manhajar su suna so su shiga kasuwar Pi ta duniya idan an fara.
Wani abun burgewa har da mutanen mu na Nigeria ta Arewa, developers da dama sun aike da aiyukan su zuwa ga Pi, suna fatan shiga cikin harkar, sai bayan abubuwa sun kankama ne zaka yi mamakin wadanda zaka gani ko zaka ji suna cikin hidimar.
Dan haka, wadannan Applications na 'yan kasuwa da kamfanonin da zasu shiga kasuwar Pi sai an tace su, Kai ba zaka iya sanin gaskiyar su da ingancin su ba, sai Pi amince musu.
Pi Network za suyi amfani da SDK da API su ware kamfanoni na gaskiya Dana karya, sai a zuba na gaskiyar akan Pi Browser, sune aka tabbatar da ingancin su aka amince kayi hada hada dasu, domin Kai baka San kamfanonin ba, Pi ne suka San su.
Sannan kamfanonin Suma basu sanka ba, Pi suka sani, su Kuma Pi sune zasu tabbatar ma kamfanonin cewa Kai Pioneer ne, Pi din da kake dashi na gaskiya ne Mining kayi, sai su yarda su baka kaya Kai kuma ka basu Pi, kenan su Pi sune a tsakiya, sune zasu tsaya maka domin kada wani kamfani ya cuce ka.
Haka kuma su zasu tsaya ma kamfanin domin kada wani ya cuce su da sunan cewa shi Pioneer ne.
Idan wani kamfani yaje ya siyar da kayan sa ma wani ko ma wasu a wani wajen da ba Pi Browser ba toh kamfanin ta shafa, babu ruwan masu Pi, Dan haka kamfanoni zasu tsaya akan Pi Browser ne kadai, kaima ka tsaya akan Pi Browser kadai.
Domin a yanzu a dai dai wannan gabar macuta suna ta fitowa suna sace Pi din mutane da sunan an siyar musu da kaya, kwana 1 shiru, Kwana 2 shiru, sai daga baya ka gane wasu ne suka cuce ka ne, saboda baka tsaya ka fahimci me Pi suke cewa a white paper din su ba.
Idan kaje zaka ga sun tsara komai kamar Pi na gaskiya, Kuma zaka ga bayanai sosai, amma fa Pi basu san dasu ba, Dan haka Dr. Nickolas cewa idan kaje ka bayar da Pi dinka ma wani a wata hanyar ta daban ba takan Pi Browser toh at your own risk, Kai ta shafa, Kai ka jiyo, babu ruwan su.
So, mu jira Pi Network su fitar da Application din kamfanonin da suka tantance su, suka amince dasu kafin mu fara wata cinikayya ko transfer din Pi domin bayar da wani kaya ko wasu kudade.
Transactions da wasu suka yi har suka yi screenshot tabbas yayi kam, amma babu amincewar Pi, kuma ba ta kan Pi browser aka yi ba, na tabbas da ace 'yan uwa da suka yi transaction din sun San da wannan bayanin da ba zasu yi ba, Allah ya tsare gaba.
Allah yasa mu dace.......
Othman Omar Farooq.
I am sending you 1π! Pi is a new digital currency developed by Stanford PhDs, with over 33 million members worldwide. To claim your Pi, follow this link https://minepi.com Othman4340 and use my username Othman4340 as your invitation code.
No comments:
Post a Comment