Sunday, 17 July 2022

Jiya bayan gudanar da adua ga Marigayi Malam Nura Director na dauki dogon lokaci ina tunani

DARASI DAGA ADUOIN DA DATTAWAN KANNYWOOD KE JAGORANTA
Jiya bayan gudanar da adua ga Marigayi Malam Nura Director na dauki dogon lokaci ina tunani  tarayyarmu a wannan masanaanta rayuwar mu a cikin ta, wadda ta hada da muamular mu hakilon mambobi wajen neman yardda asiri zai rufu, mutuwar yan uwa bayan rayuwa, da Dai sauran abubuwa da yawa akan wannan masanaanta da ita kanta sanaar haka zuciyata tayi ta zagaye ta kulla min wannan tu tuna min wannan har saida a wata gabar ta rinka yanke min hukunci.
Yanuwana a daidai wannan lokaci zanyi Amfani da wannan dama in nusar da mu cewa lokaci fa baya jira, ya kamata mu yiwa kawunan mu karatun ta nutsu, masanaanta dai gatanan Allah ya huwace mana ga tarin Jamaa tare da fikira wadda koda yaki zamu tuatara wallahi sai anyi mana tsammanin sai Dai duk da wannan baiwar da Allah ya Bamu mun kusa Kacokal lissafi ya kwace mana.wanda ni a ganina the earlier  the better mu far a tunanin yanzu akwai ma masanaantar Kannywood, in har tana nan toh
1. Me ya faru akanta abubuwa basa gudana kamar yadda sauran masanaantu a kasar nan suke gudanar da sabgoginsu.
2. Toh menene da menene ya kamata ayi fixing ko a gyara domin inganta ta ta fuskar kasuwancin abubuwa da suka hada mu, tare da inganta tarayyar mu, muamular mu, taimakakkeniyar Juna, saita zukatanmu tare da yadda  kaddarar data hada mu tare.
3. Ta yaya zamu sake nazartar sake zamanantar da dorata akan mizanin girbar riba ba asara ba.
4. Ta yaya zamu sake saisaita zukatan dukannin yayanta akan facing reality na rayuwar Sanaa ba zaman bariki ba kamar yadda wasu ke shigowa da tunanin hakan.
Toh idan kuma tunaninmu a yanzu ya fada mana a zahiri yanzu fa babu Kannywood tunda a tunanin wasu a cikin mu abin dafa ya hada mu yanzu abubuwa sun rikita babu kasuwancin hajjar tamu, toh lalle ya zama wajibi muyi tunanin gaggawa na.
1. Yaya za ayi a maido da masanaantar Taci gaba da existing cikin girbar riba zamantakewar kasuwanci Mai tarbiyya da sauran abubuwan da suka jawo faduwar masanaantar tare da ita kanta sanaar.
Yes akwai kunguyoyi, akwai shugabanci Sannan akwai mabiya, wadannan sune tarayyar da ake rayuwar wannan masanaanta dasu wanda idan mun dube su da kyau suna nan kamar yadda sauran kungiyoyi suke Zaune akai  idan basa zaune a daidai yadda ya kamata toh menene ba daidai ba kuma yaya zaa gyara su a Dora.
Ina Mai tunasar da mu fa Cesar Kannywood fa ta tumbatsa tayi cikar da har yanzu yawancin mu mun kasa gane hakan Wanda a daidai wannan lokacin ne ya kamata muyi achieving dukkanin kudurorinmu amma sai gashi a yanzu ne mafi yawancin mu muke running shelter to shelter, dan neman abun da zamu kai Bakunan mu, yawancin mu wallahi wallahi sai mun Fito mun nema muke komawa gida mu kimtsa gida haka cikin wannan hakilon mutuwa take riskarmu, wasu idan kaje zanaizarsu tun daga nan zama fara zubar da hawaye  Wane wance ashe haka akeyi ta rayuwa toh amma daga wannan koke koken da zaman makoki da ire iren aduoin da dattawa me shiryawa shike nan an gama babu sauran bibiya lalle kaicon mu. Wasu tsiraru daga cikin mu sun samu dama hakika Allah ya Sani Sun yi kokari amma a gaskiya mafi yawancin mu suna mantawa da kaddarar data hada mu tare dan Allah a Dubi wannan Lamari a gyara.
Wannan rubutun da nayi kusan zai zame min phase one, in Allah ya yadda zan kawo phase 2 Mai taken DAN ALLAH MU DAURE KAR MU ZAMA TARON YUYU YU.




Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...