Monday, 28 February 2022

AMFANIN GANYEN GWANDA

*CUTUKAN DA GANYEN GWANDA KE MAGANI AJIKIN DAN'ADAM*

✍️✍️Anas isah Ismail

Shidai lamari na Ganyen gwanda, yana kashe cututtukan fata (kaikayi, fari, kuraje, saba) Ganyen gwanda na maganin gyambon ciki (ulcers) sai a nemo ganyen gwanda a wanke a shanya idan ya sha iska sai a daka a sanya ruwan zafi mai kyau misalin rabin cup madaidaici sai a zuba kadan a sha da safe kullum bayan an karya.

Ganyen gwanda na kashe tsutsotsin ciki (intestinal worms)

Ganyen gwanda na maganin ciwon gabobin jiki da jiyojin jikin dan adam saboda da samuwar sinadirin chymopapain.

Ganyen gwanda na warkarda cutukan ciki da kumburin ciki da matsalolin da suka shafi na hanjin ciki.

Ganyen gwanda na wanke kazamta da wani abu mai cutarwa da yaiyi laulayi a kan babbar hanzanya.(cleanse colon from toxins)

Ganyen gwanda na kawar da kwayar cutar ciwon daji(cancer cells).

Yayan gwanda (seeds)  suna kara lafiyar zuciya dan samuwar vitamin A,C da E a cikinsa masu taimakon kare afkuwar matsaloli kamar su ciwon suga dana hanyoyin jini har zuwa ga zuciya.

Ganyen gwanda nada sinadiran papain da chymopapian masu rage kumburi a sassa da dama na jikin dan adam.

Ganyen gwanda na sanya laushin bayan gari idan ya yi tauri da yawa kamar na dabbobi(constipation).

Ganyen gwanda na narkarda sinadiran cholesterol da yawansu a jiki illa ne matuka musamman ga zuciya, vitamin E da C dake a ciki suna taimakawa dan hana kitsen daskarewa akan hanyoyin jini.

Ganyen gwanda na maganin basir mai tsiro da gudawa.

Ganyen gwanda na maganin kwarnafi.

Ganyen gwanda na maganin malaria a sanadin sinadirin Acetogenin dake a cikinsa.

Ganyen gwanda na maganin ciwon hanta.

TUNATARWA
kada mai juna biyu tayi amfani da ganyen gwanda domin yana motsa mahaifa.

Yawan shan ruwan ganyen gwaiba na haifarda ko dai ganin juyuwa ko zafin ciki da makamantansu a dan haka sai a san yanda za a sha.

Ka zama likitan kanka. Ilmin da ba naka ba sai kayi kokari ka neme shi ga wadanda suke da shi dan ita lafiya kiwonta ake yi

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...