Tuesday, 28 December 2021

ILIMIN TAFIN HANNU

ASSALAMUALAIKUM YAN UWA ALMAJIRAI MASOYA ANNABI MUHAMMADU S A W MUNA ZIYARA     zamu cigaba da karatummu na tafin hannu wato علم الكف  ilimin tafin hannu (1)   zamu Fara daga yan yatsu  na hannu (KARAMIN DAN YATSA) Shi ake Kira UDARID da turanci shine  (MERCURY)  Amma bisa wannan hanya ta ilimin karanta tafin hannu saboda muhimmiyar dangantakar da take tattare tsakanin shi karamin dan yatsan da wannan shi tauraro saboda shi karamin dan yatsa shine yake nuni  dangane da hankali, wayo, dabara,hangen nesa,ko wasu abubuwa na sihirce sihirce ko falsafanci ko wata hazaka ta musamman. Idan ka dubi yatsun hannun mutum kaga cewa  karamin dan yatsansa yafi sauran yan yatsunsa kyau ko kuma Babu wani lahani daya taba faruwa a jikin karamin dan yatsansa to hakika wannan mutum zaka sameshi mai  cikakken tunani ne koda ace bayyi karatun wani   ilimi ba  zaka sameshi yanada wata wayewa da hangen nesa ire iren wadannan karamin yatsan su yake lafiyayye kuma aka Sami farcen dogo za a same su ko masu harkar magunguna  ( Irina kenan ) ko harkar kasuwanci masu ciniki daidai  ko falsafawa (phylosophers) ko  masana taurari ko masu koyarwa ko lauyoyi ko masuyin ramuwa cikin ruwan sanyi  shi wanna karamin dan yatsan  yanada babban matsayi  acikin sauran yan,yatsun. Idan ka duba koda kirge zakayi da sauran yan,yatsunka  ta kansa zaka fara kowani dan yatsa zaka sameshi yanada gaba guda uku gaba ta farko ta karamin dan yatsa wato gaba da farce take tare da ita. Itace gabar da take nuni bisa hankali ta mai hannun . Idan kaga wata illa,ko wani tabo ko wani abu ya faru akan wannan gabar rauni ko konewa. Yana nuna cewa mutumin zai zama mai saurin damuwa akan Abu karami ko babba idan kuma aka Sami rauni  ajikin farcen karamin yatsa na hannun dama. Wannan Yana nuna mutumin yanada makiya da yawa maza da mata musamman daga cikin yan uwansa da makobtansa Amma babu abinda zai cuceshi. Gabar tsakiya ta karamin dan yatsa idan an sameta kafiyayya tana nuna mutumin zaifi karfin abinda zaici da abinda zaisha da wurin zama  wato zai zama mawadaci mai mutunci a idon jama a kuma daga wannan gaba ta tsakiyar karamin dan yatsa ake gano tsawon ran mutum ko yadda rayuwar sa zata kasance. Gaba ta uku ta karamin dan yatsa itace gabar iyalinsa  da hurdarsa ta cikin gida karamin dan yatsa shine yake nuni da ranar laraba ranarsa kenan. T Alhmdllh lillahi muhadu a karatun gaba daga Taskar asirai malam basiru taraba stete jalingo




Sunday, 26 December 2021

SIRRIN DA AKEYI ACIKIN WANNAN SHEKARA DOMIN SAMUN SAUKIN RAYUWA DA SAMUN...

BINCIKEN TAFIN HANNU

ASSALAMUALAIKUM YAN UWA ALMAJIRAI MASOYA ANNABI MUHAMMADU S A W MUNA MUKU SALLAMA IRIN TA ADDININI MUSULUNCI BAYAN HAKA YAU 25/12/2021 ZAMU FARA KARATUN علم الكف ILIMUL KAFFI AMMA ZAMU FARA DAGA LITTAFIN SHEHIN MALAMI SHEIKH HUSAIBAKAR. RTA MAI SUNA HANNUNKA SIRRINKA DAGA NAN IDAN MUKA GAMA ZAMU SHIGA MANYAN LITTATAFAN ILIMUL KAFFI DOMIN NEMAN ADDUAR KIRKI DAGA MUTANEN KIRKI ...........................................................= TAKAITACCEN TARIHIN DUBAN TAFIN HANNU WANDA AKE KIRA (PALMISTRY) DA TURANCI. shi wannan fanni muhimmi ne da gaske, wanda shekaru da yawa da suka gabata ake yin amfani dashi. Kuma idan aka zurfafa bincike gameda lokacin da aka fara amfani dashi. Za aga cewa tun kafin Annabi daidai (A.S) ake amfani dashi. Domin ansamu wani kwararren masanin wannan fanni Wanda ake Kira (FASUTA) Wanda yake tare da ( JALUTA) Domin an samu sanda JALUTA ya fito yaki da TALUTA.sai da FASUTA ya duba tafin hannun JALUTA. Bayan ya duba yake cewa dashi.yajanye fita yakin Sai wani lokaci domin idan ya fita yakin da kyar zai dawo JALUTA yaki karbar shawarar daya fita yakin bai dawo ba Annabi dauda (A.S) alokacin Yana daga cikin sojojin taluta shine yasamu nasarar kasheshi. Hakika shi wannan fanni ilimin da ake Kira (PALMISTRY) a turance ilimi ne da yake nuna ikon Allah da tsarinsa kamar yadda ya banbanta wa mutane. Kamannisu.da Muryarsu . Halayensu . To haka shi wannan ilimi ya Fara bunkasa daga kasar syria sannan. Girkawa suka karba suka yita bincike akansa sannan kasar india ta karba sannan kasar egypt masar ta karba sannan kasar china ta karba wannan tsawon lokaci da ya gabata kenan Wanda kusan a yanzu a kasashen turai da Asiya da kudancin amurka da arewacinta. Da wuya kaje wata kasa ko wani babban gari baka samu kwararrun masana akan wannan fanni ba. Anyi rubuce rubuce da yawa akan wannan fanni cikin manyan harsunan duniya kamar english da faransanci harshen mutan kasan sin wato china da italiya da jamisanci da larabchi to Alhmdllh lillahi muhadu a karatun na gaba daga Taskar asirai malam basiru taraba stere jalingo

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...