ASSALAMUALAIKUM YAN UWA ALMAJIRAI MASOYA ANNABI MUHAMMADU S A W MUNA ZIYARA zamu cigaba da karatummu na tafin hannu wato علم الكف ilimin tafin hannu (1) zamu Fara daga yan yatsu na hannu (KARAMIN DAN YATSA) Shi ake Kira UDARID da turanci shine (MERCURY) Amma bisa wannan hanya ta ilimin karanta tafin hannu saboda muhimmiyar dangantakar da take tattare tsakanin shi karamin dan yatsan da wannan shi tauraro saboda shi karamin dan yatsa shine yake nuni dangane da hankali, wayo, dabara,hangen nesa,ko wasu abubuwa na sihirce sihirce ko falsafanci ko wata hazaka ta musamman. Idan ka dubi yatsun hannun mutum kaga cewa karamin dan yatsansa yafi sauran yan yatsunsa kyau ko kuma Babu wani lahani daya taba faruwa a jikin karamin dan yatsansa to hakika wannan mutum zaka sameshi mai cikakken tunani ne koda ace bayyi karatun wani ilimi ba zaka sameshi yanada wata wayewa da hangen nesa ire iren wadannan karamin yatsan su yake lafiyayye kuma aka Sami farcen dogo za a same su ko masu harkar magunguna ( Irina kenan ) ko harkar kasuwanci masu ciniki daidai ko falsafawa (phylosophers) ko masana taurari ko masu koyarwa ko lauyoyi ko masuyin ramuwa cikin ruwan sanyi shi wanna karamin dan yatsan yanada babban matsayi acikin sauran yan,yatsun. Idan ka duba koda kirge zakayi da sauran yan,yatsunka ta kansa zaka fara kowani dan yatsa zaka sameshi yanada gaba guda uku gaba ta farko ta karamin dan yatsa wato gaba da farce take tare da ita. Itace gabar da take nuni bisa hankali ta mai hannun . Idan kaga wata illa,ko wani tabo ko wani abu ya faru akan wannan gabar rauni ko konewa. Yana nuna cewa mutumin zai zama mai saurin damuwa akan Abu karami ko babba idan kuma aka Sami rauni ajikin farcen karamin yatsa na hannun dama. Wannan Yana nuna mutumin yanada makiya da yawa maza da mata musamman daga cikin yan uwansa da makobtansa Amma babu abinda zai cuceshi. Gabar tsakiya ta karamin dan yatsa idan an sameta kafiyayya tana nuna mutumin zaifi karfin abinda zaici da abinda zaisha da wurin zama wato zai zama mawadaci mai mutunci a idon jama a kuma daga wannan gaba ta tsakiyar karamin dan yatsa ake gano tsawon ran mutum ko yadda rayuwar sa zata kasance. Gaba ta uku ta karamin dan yatsa itace gabar iyalinsa da hurdarsa ta cikin gida karamin dan yatsa shine yake nuni da ranar laraba ranarsa kenan. T Alhmdllh lillahi muhadu a karatun gaba daga Taskar asirai malam basiru taraba stete jalingo
No comments:
Post a Comment