YAYA ALAƘARKI TAKE DA ALƘUR'ÃNI A CIKIN WATAN RAMADANA?
.
🍂 Shin wacce irin alaƙa kika ƙulla da alƙur'ani mai girma a cikin wannan watan na Ramadana mai albarka, kina karantashi ne ko kuma kin nesanta daga gareshi? to kodai a wane hali kike, kada ki kuskura aikace-aikacen cikin gida su haneki daga karantashi ko kuma sauraronsa koda na ƴan lokuta ne.
🍂 Da yawan wasu matan, zaka samesu a zaune a cikin gida, babu abinda suke yi na daga aikace aikace sai kalle-kallen fina-finai kawai, basa karanta alƙur'ani ko sauraronsa, sun nesanta daga gareshi alhalin kuma ana son a kusanceshi musamman ma a cikin wannan watan mai albarka.
🍂 Ki zanto kinyi amfani da rarar lokacin da kike dashi wajen karatun alƙur'ani mai girma a cikin gidanki, koda kin kasance a cikin kicin kike, idan kuwa babu damar karantashi ɗin, to ki daure ki zanto daga cikin masu yawan saurãren ƙira'ar alƙur'ani a cikin wannan watan mai albarka na Ramadan
KADA KAYIWA ANNABI ﷺ ƘARYA!
.
🍃 Yiwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ƙarya ba kamar yiwa sauran mutane ƙarya bane
🍃 Abin zai baka mamaki da kuma haushi, musamman akan yanar gizo ta zamani, sai kayi ta ganin ana yaɗa ƙarya akan annabi, ace yace abu kaza alhalin kuwa bai faɗa ba, suna ta bada fatawa ba tare da dalili ba, subhanallah inama dai mutanena sun gane!
🍃 Yiwa Manzon Allah ﷺ ƙarya tamkar halakar da kaine, domin haƙiƙa duk wanda yake yi masa ƙarya da gangan, to lallai yana gina gidan zamansa ne a cikin wuta sakamakon wannan ƙaryar tasa.
🌴Manzon Allah ﷺ yace: *"duk wanda yayi min ƙarya da ganganci, to lallai ya tanadi wurin zamansa daga cikin wuta"*
📒 Jami'i At-tirmiziy (2669)
🍃 Da haka ne zaka gane cewa lallai fa yiwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ƙarya ba ƙaramin laifi bane, domin yi masa ƙarya cikin wuta take tunkuɗa mutum matuƙar da gangan yayi ta kuma bai tuba ba.
ME KAKE YI DA AZUMIN NAN?
.
🍂 *Shin mene ne ya kasance aikin yinka wanda kafi baiwa muhimmanci a cikin watan azumin nan?*
👉🏻 Karatun alƙur'ani mai girma, ko kuma na boko, ko kuwa na littattafan musulunci da nazari a cikinsu?
👉🏻 Ko kuma kalle-kallen shirme na fina-finai ka kasance kana aikatawa a cikin wannan watan mai albarka.
👉🏻 Ko kuma dai bacci kawai ka kasance kana baiwa lokacinka.
🍂 Haƙĩƙa babu wani aiki mafi soyuwa a cikin wannan watan na Ramadana fiye da karatun alƙur'ani mai girma, da salloli akan lokutansu, da kuma dukkanin dangogin aiyukan ɗa'a ga Allah swt.
🍂 Kada ka kasance mai ɓata lokacinka a cikin wannan watan mai albarka na Ramadana ta hanyar kalle-kalle da karance-karance marasa amfani a gareka.
🍂 Ka duƙufa wajen aikata ayyukan alkhairi a rayuwarka, musamman ma a cikin wannan watan mai albarka, kada ka banzatar da lokacinka a banza ba tare da ka kasance kana aikata wani kyakkyawan aikin da zai kusantaka da ubangijin taliƙai ba.
No comments:
Post a Comment