Wednesday, 30 March 2022

SALLAR TUBA GA ALLAH





SALLAR TUBA GA ALLAH

An ruwaito daga Abubakar Assiddeeq (RA) ya ce: Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Babu wani bawa da zai aikata wani zunubi, sai ya kyautata alwala, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, sai ya roki gafaran Allah face Allah ya gafarta masa, sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sai su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane". 
Abu Dawud ya ruwaito, Albaniy ya ingantashi.

💦

Yana daga cikin rahamar Allah ga bayinsa bude kofar tuba a garesu wacce ba ta yankewa har sai in an zo gargarar mutuwa ko idan rana ta fito daga mafadarta.

Sababin wannan sallar shine: idan mutum ya fada cikin zunubi babba ko karama, to lallai yana wajaba a gareshi da ya gaggauta tuba ga Allah, bayan nan an so yayi wannan raka'oi guda biyu, wato mutum ya aikata wani aikin da'a don samun kusanci ga Allah, yayi tawassuli da ita ga Allah yana mai fata da kwadayin Allah ya karbi tubansa ya gafarta masa zunubansa.

●LOKACIN YIN TA:

Mustahabbi ne yin wannan sallah a lokacin da mutum yayi azamar tuba daga zunubin da ya aikata, nan take ne yayi zunubin ko kuwa an dauki lokaci da ya aikata zunubin, Ita wannan sallah an shar'anta yin ta a kowane lokaci har a lokutan da a ka hana yin nafila, saboda ita sallah ce da take da sababi, don haka an shar'anta ta duk a ka samu sababinta.

●SIFAR SALLAR TUBA

•Sallah ce nafila raka'a biyu.
•Mutum zai sallace ta shi kadai ba a jam'i ba.
•Mutum zai karanta abin da ya sawwaka mishi na daga Alkur'ani.

●Mutahabbi ne ga wanda ya tuba daga wani zunubi to ya dage da aikata ayyuka na kwarai, saboda fadin Allah:

"وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ اهْتَدَىٰ". (طـه :82) 

"Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa".

●Mafi falalar wadannan ayyuka da mai tuba zai yi shi ne: SADAKA, domin sadaka tana daga cikin manyan sabubban da suke kankare zunubai, Allah Madaukaki ya ce:

"إِن تُبْدُوا الصَّدَقَاتِ فَنِعِمَّا هِيَ ۖ وَإِن تُخْفُوهَا وَتُؤْتُوهَا الْفُقَرَاءَ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّئَاتِكُمْ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ"
(البقرة :271) 

"Idan kun bayyana sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa daga barinku daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne".

Kuma ya tabbata a hadisin Ka'ab bn Malik (RA) cewa, a lokacin da Allah ya karba tubansa ya ce: Ya Manzon Allah yana daga cikin cikan tubana in bayar da dukiyata sadaka ga Allah da Manzonsa, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: ka rike wani yanki na dukiyarka don alkhairi ne a gareka...". Muttafakun alaihi.

Allah ya azurtamu da yin ingantacciyar tuba, tuban da ba za mu sake komawa ga wannan zunubin ba.












Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...