Monday, 7 March 2022

QALUBALE GA DUKKAN BATIJJANE !!!*

*QALUBALE GA DUKKAN BATIJJANE !!!*

*⌛DABARAR YAN SHI'AH NA SHIGOWA CIKIN TIJJANAWA, DA YAUDARARSU DA KARBAR DARIQAR TIJJANIYYA DON SUYI AMFANI DASU WAJEN CUSAWA MASU KARANCIN ILIMINSU AQIDAR SHI'AH BA TARE DA SUN SANI BA⌛*

*KASHI NA FARKO:*

*MAUDHU'I: MENENE YASA YAN SHI'AH SUKA ZABI SHIGA CIKIN TIJJANAWA AKAN SAURAN DARIQU DA AQIDUN DA MUKE DASU A AFRICA ?*


*Muna fara wannan rubutu da sunan mamallakin halitta baki daya. Wanda ya samar da samuwa don a bisa zabinsa, ya kuma saukar da tsarin da yake so halittunsa su kasance akansa. Tsira da amincin allah su kara tabbata ga shugaban samammu, wanda allah ya samar da halitta saboda bayyanar da girmanshi da isarsa a wajenshi, wato annabi muhammadu (s.a.w). Allah kasa da ahalinsa madaukaka, da sahabbansa masu girma, da duk wadanda suka biyo bayansu da kyautata ayyuka cike da tsarkin zuciya har izuwa ranar karshe.*


*GABATARWA:*

*Hakika munyi zurfin tunani, da nazari, hade da duba da bincike akan abinda yake nema ya rikita tsarin tafiyar Yan darikar tijjaniyyah a wannan lokaci da muke ciki, ta yanda muka ga yadda Samarin darikar tijjaniyyah da yawa suna sauka daga tarbiyyar dariqar tijjaniyyah izuwa aqidun shi'ah ba tare da sun sani ba, harma suna daukar hakan a matsayin burgewa da cinyewa a cikin tafiyar darikar tijjaniyyah. Hakan yasa samarin da suke cikin wannan matsala firgicewa da sambatu na maganganun da basu da tushe bare makama a cikin darikar tijjaniyyah.*


*MAUDHU'I: MENENE YASA YAN SHI'AH SUKA ZABI SHIGA CIKIN TIJJANAWA AKAN SAURAN DARIQU DA QUNGOYOYIN ADDININ MUSULUNCI DAKE AFRICA ?*

*Hakika duk wanda ya san qididdiga da kiyasin mutanen africa musulmai dole zai san babu musulman da suka fi yawa kamar yan darikar tijjaniyyah. Sannan babu mutane masu saurin yarda da wankakkiyar zuciya kamar tijjanawa. Duk wanda yace yana son annabi (s.a.w) zasu soshi, kuma zasu iya yi masa komai yake so matukar basu ga sabawa umarnin allah akan hakan ba. Sannan basu da mummunan zato ga duk wanda ya bayyana musu kyakykyawan abu. Abinda ka bayyana musu shi zasu dauka musamman idan abun mai kyau ne, ba zasu biyo bayanka da zargi ko tuhuma akan abinda ka bayyana musu na kyakykyawan furuci ko aiki.*

*Wadannan abubuwa sune suka zamo lagonsu da duk mai son cutar dasu ko yaudararsu yake amfani dasu matukar ya sansu. Sun san da wannan, kuma sun san ana amfani da hakan wajen cutar dasu amma basu canja ba daga wannan kyakykyawar zuciya tasu.*


*MAFARIN ZANCE:*

*Hakika Yan shi'ah mutane ne masu fadada bincike da iya tsari, da kuma yin dogon shiri don cimma muradinsu. Suna iya rikidewa izuwa kowace siffa, sannan suna iya daukar tsawon lokaci suna shirya shirinsu na makirci akan wanda suke so suyi nasara akansa. Sannan suna da kokarin yin karatu don ya zamo musu makami wajen samun nasarar shawo kan mai mai karamin sani dangane da lamuran addini.*

*Hakika sunyi nazari akan tijjanawa sosai. Kuma duk awonsu yayi daidai da bukatarsu.*

*Basu da karfin jama'ah na zahiri da kuma yardar mutanen gari, da zasu iya yin amfani dasu wajen yada da'awarsu ta shi'ah. saboda haka; Suna son su samu karfin jama'ah, sannan kuma su samu wadanda zasu yarda dasu ba zasu koresu daga garesu ba, sannan wadanda zasu amince su mu'amalancesu da zuciya daya ba tare da zargin akwai wata manufa a karkashin zuciyarsu ba da suke son isarwa. saboda haka sai suka duba suka ga wadanne musulmai ne masu yawan da zasu iya rabuwa dasu don su samu karfi daga karfinsu, sannan su shigar da akidunsu cikinsu ba tare da sun sani ba ?*

*Sai suka ga tijjanawa ne suka fi kowa yawa a africa, Hakane yasa suka zabi shigowa cikin dariqar tijjaniyyah don tijjanawa su yarda dasu, su dauka tare suke dasu. Don su saki jiki dasu. Sannan idan wani zai kawo musu hari tijjanawa su zama garkuwarsu. Sannan su samu damar shiga guraren da a baya basu isa su shigesu ba saboda ba'a yarda da akidarsu a wajen ba. Amma ra'buwarsu da darikar tijjaniyyah sai ya zama sun shiga wajen da lasisin darikar tijjaniyyah. Ta hakan sai suyi da'awar tijjaniyyah kunshe da manufar isar da akidojin shi'ah ga mutanen da basu san kansu ba.*

*Wannan shine dalilin da yasa Yan mazhabar shi'ah suka zabi shiga darikar tijjaniyyah akan sauran dariku da qungiyoyin addini da suke africa.*



*ZAMU DORA A RUBUTUNMU KASHI NA BIYU INSHA ALLAH.*

*INDA ZAMU JI MENENE YAN SHI'AH SUKA FARA YI KAFIN SU FARA ISAR DA MANUFARSU A CIKIN TIJJANAWA, DON NEMAN YARDAR TIJJANAWA, BAYAN SUN SHIGO DARIQAR TIJJANIYYAH ?*

*RUBUTUNMU KASHI NA BIYU ZAI ZO ANAN KUSA INSHA ALLAH.*

No comments:

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...