MUHADARA TA MUSAMMAN KAN AZUMI
Kashi Na 1
Abu Na Farko 'Yan Uwa Shi Addini Tsari Ne Na ALLAH Subhanahu Wata'ala Ba Malamai Ne Suka Zauna Suka Tsara Addini Ba ALLAH Ya Shar'anta Shari'a Da Kansa Ɗaya Daga Cikin Manufofi Shar'anta Addini Wa Bayi Shine Tausayi Da Jinƙan ALLAH Akan Su Bayi Soyayya Da Ƙauna
Idan Badin Hakaba ALLAH Bashida Riba Ko Faɗuwa Wajan Shar'anta Addini
Ya Tabbata Acikin Hadisin Qudusi Al'imamu Muslim Ya Fidda Hadisin Hadisin Abu Zalrilgifari
ALLAH Subhanahu Wata'ala Yake Cewa;
"Yaa Ku Bayina Inda Na Farkon Ku Har Zuwa Na Karshen Ku Aljanin Ku Da Mutanen Ku Duk Ku Daidaita Akan Zuciyan Mafi Tsoron ALLAH Cikin Ku Annabi Yakan Ce Nafiku Tsoron ALLAH Nafiku Bin ALLAH Sau Da Ƙafa Idan Da Kowa Bin ALLAH Sa Ɗa'a Ma ALLAH Da Bin Dokokin ALLAH Sa Kamar Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wa Sallam Yake Wannan Baze Daɗeni Da Komai Ba ALLAH Yace Bazan Karu Da Komai A Iko Naba"
"Yaa Ku Bayina Inda Na Farkon Ku Har Zuwa Na Karshen Ku Aljanin Ku Da Mutanen Ku Duk Ku Daidaita Akan Zuciyan Mafi Fajircin Cikin Ku Rashin Imanin Sa Da Rashin Arzikin Sa Kamar Fir'auna Yake Ko Abu Jahalin ALLAH Yace Bazan Cutu Da Komai Ba"
In Duk Kowa Zai Lalace Kowa Zai Lalace Ace Bazebi ALLAH Ba Bazeyi Imani Ba ALLAH Yace Nifa Bazan Rabu Da Komai Ba Waɗannan Jimloli Sakon Dasuke Isar Mana Duk Wadda Kaga Ya Riƙe Addini Ya Riƙe Imani Ya Riƙe Nagarta Yafa Riƙe Ne Ma Kansa Wadda Yayi Watsi Da Addini Yayi Watsi Da Shari'a Ya Juya Baya Ma ALLAH Da Dokokin ALLAH Yayi Ne Ma Kansa Wannan Shine Ƙa'ida Na Farko Daya Kamata Ka Fahimta
Ladan Da Yake Kiran Sallah Yana Kirane Ma Kansa Liman Da Yake Jan Sallah Yana Jan Sallah Ne Ma Kansa Inkaga Mutum Na Karanta Alqur'ani Yana Karantawa Ne Ma Kansa ALLAH Bashida Riba Ko Faɗuwa Akan Kayi Koba Kayi Ba
🎤🎤🎤
Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Muhaɗu Kashi Na Gaba
🙏🙏🙏
No comments:
Post a Comment