FIFIKON ANNABI AKAN AL'UMMAH (2)
Salati Marashin Farko da Qarshe da tasleemi mafi cikar cika su tabbata bisa Mafi Girman dukkan bayi awajen Allah, Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa Haskaka da Sahabbansa Shiryayyu da dukkan Nagartattun bayinsa har zuwa ranar da Qasa ke fidda nauye-nauyen cikinta.
8. Yana daga cikin kebantuwar darajarsa cewa shi ka'dai ne Ummiyyi acikin Annabawa (alaihimus salam) wato ba ya karatu ko rubutu amma kuma dukkan wani mai ilimi daga hasken iliminsa ya 'dosana.
9. Yana daga cikin kebantuwar darajarsa kasancewar acikin littafinsa (Alqur'ani) akwai ayoyin dake shafe hukuncin wasu ayoyin. Amma sauran Annabawa basu samu wannan ba.
10. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa shine Cikamakin dukkan Annabawa da Manzanni (alaihimus salam) Shine mafi darajarsu kuma shine Qarshen aike ﷺ
11. Yana daga kebantuwar darajarsa kasancewar Shari'arsa dawwamammiya ce har zuwa tashin Alqiyamah, Kuma addininsa ya shafe dukkan addinai da shari'o'in da suka zo kafinsa.
12. Yana daga cikin kebantuwar darajarsa cewa an bashi ayoyin Qarshen suratul Baqarah ne daga wata taska dake Qarkashin Al'arshi.
13. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa shi kadai aka bama Suratul Fatiha wacce ita ce Sab'ul Mathaniy. Kuma ba'a ta'ba bama wani Annabi kafinsa ba.
14. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa an aikoshi ne zuwa ga dukkan mutane baki daya. Bakakensu da fararensu, da larabawa da baibayi, da kuma dukkan Aljanu baki daya.
15. Yana daga kebantuwar darajarsa kasancewarsa shine wanda yafi dukkan Manzanni yawaicin mabiya.
16. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa bai ta'ba yiwa Allah laifi ba. Kuma duk da haka Allahn ya yafe masa abinda ya gabata da kuma abinda ya jinkirta.
17. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa shi ka'dai Allah ya bama tafkin nan na Alkauthara. Wanda ruwansa yafi Madara haske, yafi zuma zaqi, kuma yafi Qankara sanyi da da'di.
18. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa shi ka'dai ne Annabin da Allah ya aika zuwa ga dukkan Aljanu baki daya. Kuma yaje yayi wa'azi agaresu har ma wasu da yawa sunyi imani dashi daga cikinsu.
19. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa tafkinsa na Alkauthara yafi dukkan tafkunan Annabawa girma da kuma yawan masu sha.
20. Yana daga kebantuwar darajarsa cewa Allah Madaukakin Sarki ya bashi rundunonin Mala'iku suna tayashi Yaqi a yakokinsa ﷺ
Salati da amincin Allah su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa bisa gwargwadon yawan dukkan Salatai da tasleemai da aka ta'ba yi gareshi
No comments:
Post a Comment