Tuesday, 29 March 2022

*SHAN AZUMIN MAI CIKI DA MAI JEGO: RAMUWA KO CIYARWA?*

*SHAN AZUMIN MAI CIKI DA MAI JEGO: RAMUWA KO CIYARWA?*
.
.
Abu na farko da ya kamata a sani cewa, ba ya halasta ga mai ciki ko mai jego ta sha azumi don kawai tana da juna biyu ko tana shayar da jariri. Sai dai in akwai tsoron cewa azumi zai iya cutar da lafiyarta ko ya jawo mata matsala ita kanta ko danta ko kuma su duka biyun. Idan ya tabbata cewa in ta yi azumi akwai matsala, to a lokacin ne ya halasta ta sha azumi.
Malamai sun yi sabani game da hukuncin mace mai ciki ko mai jego in ta sha azumi, shin ramawa za ta yi ko ciyarwa ko kuma duka biyun? Akwai maganganu malamai kamar haka.
.
.
MAGANA TA FARKO
Abu Hanifah da Ibrahim Annakha’iy suna da ra’ayin cewa abin da ke kanta shine ramuwa kawai. Wannan kuma shine mazhabar Aliyu Dan Abu Dalib (Allah ya qara masa yarda).
MAGANA TA BIYU
In mace mai ciki ko mai shayarwa ta sha azumi saboda tana tsoron lafiyarta za ta rama ne kawai. In kuma ta sha ne saboda tsoron lafiyar danta da/ko abin da ke cikinta to za ta rama tare da ciyarwa. Wannan ita ce maganar Maliku da Sufyan da Shafi’iy da Ahmad Bn Hanbal. Hakanan kuma Al-Jassas ya hakaito irin wannan fatawa daga Abdullahi Dan Umar (Allah ya qara musu yarda) Haka nan ma Maliku ya hakaito a Muwadda daga Ibn Umar din.
 .
.
MAGANA TA UKU
In mace mai ciki ko mai shayarwa ta sha azumi abin da ke kanta shine ciyarwa kawai, babu ramuwa. Ibn Abbas (Allah ya qara musu yarda) shine ke da wannan ra’ayin cikin sahabbai. Haka nan kuma Ibn Qudamah ya hakaito irin wannan magana daga Ibn Umar (Allah ya qara musu yarda).
MAGANA TA HUDU
Mai shayarwa in ta ji tsoro saboda jaririnta to za ta sha ruwa sai ta ciyar. Mai ciki kuma in ta sha za ta rama ne; domin ta fi kama da maras lafiya. Wannan shine mazhabin Alhasan Albasariy.
 .
.
MAGANA TA BIYAR
Idan mai ciki ko mai jego ta sha azumi to ciyarwa ne akanta ba bu ramuwa, amma tana da zabin ta rama ba tare da ciyarwa ba. Wannan ita ce maganar Ishaq Dan Rahwuya.

Almubarakfuriy ya naqalto maganar Ibn Hajrin a inda yake cewa: “An yi sabani game da mai ciki da mai shayarwa da kuma wanda ya sha azumi saboda tsufa in ya sami qarshin ramawa daga baya. Shafi’iy ya ce: za su rama kuma su ciyar, Auza’iy da mutanen Kufa suka ce ramuwa ce kawai akan su banda ciyarwa”. Sa’annan ya ambaci maganganun malamai mabambamta sannan ya ce: “Abin da ya bayyana gare ni shine cewa mai ciki da mai shayarwa suna daukan hukuncin maras lafiya ne da matafiyi. Allah shine mafi sani”.

Haka nan Ibn Qudama ya hakaito maganganun malamai da hujjojin su akan mas’alar sannan ya tabbatar da cewa abin da yake ganin shine daidai shine ramuwa ce akan matar da ta ji tsoro don kan ta, da kuma ramuwa da ciyarwa a kan wacce ta ji tsoro saboda kan ta da kuma yaronta.
Ibn Bazz ya fadi cewa: “da mai ciki da mai shayarwa [in sun sha azumi] hukuncinsu shine irin hukuncin maras lafiya. Saboda haka in sun kasa yin azumi za su rama daga baya. Wasu malamai kuma sun tafi izuwa ga cewa ciyarwa za su yi, amma wannan magana ce mai rauni. Abin da yake daidai shine ramuwa ce akan su kamar yadda take kan maras lafiya da matafiyi idan sun sha azumi”. Sannan ya kara cewa: “abin da yake daidai shine mai ciki da mai jego in sun sha azumi su rama. Abin da aka ruwaito daga Ibn Abbas na cewa ciyarwa ce kawai a kansu wannan zance ne mai rauni kuma ya saba wa dalilai na shari’a…”.

A cikin fatawar majalisar qoli ta malaman kasar Saudia sun ce: “In mace mai ciki ko mai sharyarwa ta ji tsoron abin da zai faru gare ta ko ga dan ta sai ta sha azumi to ramuwa ne akan ta, hukuncin daya ne da hukuncin maras lafiya wanda ya kasa yin azumi saboda tsoron cutarwa ga kansa. Allah ya ce: (Kuma wanda daga cikinku ya kasace ba shi da lafiya ko kuma yana halin tafiya [in ya sha azumi] to ya rama adadin kwanakin da ya sha daga baya [Baqara, 185])”. Sannan suka sake cewa: “Ita kuwa mai ciki, ya wajaba akan ta tai azumi sai dai in ta ji tsoron cewa azumin zai cutar da ita ko ya cutar da abin da ke cikinta, to anan an yi mata rangwame ta sha azumi, sannan ta rama bayan ta haihu ta kuma kuma tsarkaka daga jinin biqi….











Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

KUNDIN SIRRUKAN LI'ILAFI-QURAISHIN

Thursday, 24 March 2022

TASRIFIN ZOBE MAI FIDDA KUDI MANYA

MENE NE AZUMI...?? 1. AZUMI A LUGGA

 
MENE NE AZUMI...??

1. AZUMI A LUGGA
Shine kamewa
2. ASHARI'ANCE:- Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

RUKUNAN AZUMI

1. Yin niyya 

2. Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali 
3. Zamani (lokachin yin azumi).

SUNNONIN AZUMI 
1. Gaggauta buda baki
2. Jinkirta sahur 
3. Addu'a yayin buda baki
4. Yin sahur da jinkirta shi.

MAKARUHAN AZUMI
1. Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
2. Sumba
3. Dauwamar da kallo na sha' awa 
4. Tunani akan al'amuran saduwa
5. Shafa ko runguma 
6. Dandanan wani abu
7. Sanya tozali
8. Yin kaho.

ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI
1. Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
2. Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
3. Saduwa ta hanyar tilasta
4. Chi ko sha da tunanin sauran dare
5. Chi ko sha da gangan
6. Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi 
7. Ridda.

ABUBUWAN DA SUKE HALAS
1. Yin asiwaki
2. Sanyaya jiki da ruwa 
3. Tafiya ta halas
4. Sanya magani wanda ya dache
5. Tauna wani abu ga karamin yaro
6. Sanya turare.

ABUBUWAN DA AKAYI RANGWAME
1. Hadiye yawu
2. Rinjayen amai da magwas 
3. Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
4. Kuran kan hanya 
5. Wayan gari da janaba
6. Yin mafarki da rana

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.





Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Wednesday, 23 March 2022

SAMUN IJABA TAKE

787
 .
Aslm bayin Allah masoya annabi S, a, w,
.
Ga alkawarin sirrin samun ijaba mai qarfi sosai 
.
.
Ranar lahadi ake farawa  har kwana 7
.
Ana rubuta شيجكذيش  kafa 777 idan aka wanke sai rubutun saika saka gaushi mai wuta acikin rubutun saika shanye take.. Saikayi wuridin.ya shaijakaziyshu.qafa 1000 to haka zakana yi  zuwa kwana, 7 to wllh idai kayi hakan  to insha allahu duk aikin dakayi zaka sami ijaba  cikin gaggawa mujarrabun sahihun  lashakka fiyhi
SIRRI





Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Sunday, 20 March 2022

LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA

LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA


Abdullahi bn Almubarak (rah) yana daga cikin magabata na kwarai, kuma mutum ne Salihi. 

Wata shekara bayan yayi niyyar tafiya aikin Hajji, sai ya fita domin yin ban-kwana da abokansa (Almajiransa) kafin tafiyarsa. Amma akan hanyar ne yaga wani abu wanda ya tada masa hankali ya firgitashi. 

Ya hangi wata baiwar Allah tana tone juji (bola) tana tonowa wani MUSHEN KAZA wacce aka jefar. Ta daukota ta sanya a Qasan hammatarta, ta juya ta tafi aboye acikin duhu. 

Sai yayi kiranta yace "Mai kikeyi ya ke baiwar Allah?!". Sai tace "Ya kai bawan Allah,  kyale halittu da mahaliccinsu. Domin Allah yana da sha'ani acikin lamarin halittunsa".

Sai Ibnul Mubarak yace mata "Ina yi miki magiya don girman Allah ki gaya min labarinki".

Sai matar tace masa "Amma wallahi ba don ka riga kayi mun magiya ba, da ban gaya maka halin da nake ciki ba".

Kafin ta fara gaya masa har hawaye ya fara zuba daga idanunta. Sai tace "Hakika mu Allah ya halatta mana cin mushe. Domin ni Bazawara ce Matalauciya. Kuma (ni) mahaifiyar 'ya'ya mata ne guda huɗu".

"Mutuwa ta dauke Mahaifinsu mai kula dasu, Yanayi ya tsananta garemu, kuma dukiya ta Qare daga gareni. Kuma na kwankwasa kofofin mutane (wato na bibbi gidajen jama'a) amma ban samu wata zuciya mai tausayi daga wajensu ba".

"Sai na fita domin nemowa abinci ga 'Ya'yana wadanda wutar yunwa ta riga ta Qone musu hanta. Sai Allah ya azurtani da samun wannan mushen kazar da kake gani. Shin zakayi jayayya dani ne akanta?".

Daga jin wannan labari nan take sai Idanuwan Ibnul Mubarak suka rika zubda hawaye. Sai yace mata "Karbi wannan amanar". 

Sai ya damka mata dukkan dunkiyar da yayi niyyar tafiya aikin hajjin nan da ita. 

Sai Uwar marayun nan ta karba ta juya wajen 'ya'yanta tana godiya. Shi kuwa Ibnul Mubarak ya juya zuwa gidansa. Alhazai na garinsu kuma suka tafi suka sauke faralinsu sannan suka dawo. 

Amma abin mamakin duk da cewar shi bai je aikin Hajji ba, amma duk Alhazan sun dawo suna yin godiya gareshi bisa hidimar da yayi  musu awajen aikin Hajji. 

Suan cewa "Allah yaji Qanka Ya Kai Ibnul Mubarak! Babu wani wajen zama da muka zauna fache sai ka bamu wani abu daga ilimin da Allah ya sanar dakai. Kuma bamu ga wanda ya fika wajen bautarka ga Allah Ubangijinka ba, awajen aikin Hajjin nan na wannan shekarar".

Sai Ibnul Mubarak yayi mamaki kuma hankalinsa ya tashi game da al'amarinsa, da kuma al'amarinsu. Shi dai bai bar garinsa ba (ballantana ace har an ganshi awajen aikin Hajji). Kuma shi ba yaso ya bayyanar musu da sirrinsa. (wato ba yaso ya gaya musu cewar yayi sadaqah ne da kudinsa). 

To da ya kwanta barci sai yaga wani kyakkyawan mutum wanda haske ke fita daga fuskarsa. Yana ce masa "AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGAREKA YA KAI ABDULLAHI. SHIN BAKA SAN KO NI WANENE BA? AI NINE MASOYIN NAN NAKA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW) NINE MASOYINKA ADUNIYA DA LAHIRA, KUMA NINE MAI CETONKA ARANAR LAHIRA. ALLAH YA SAKA MAKA DA ALKHAIRI BISA ABINDA KAYI MA AL'UMMATA".

"YA KAI ABDULLAHI 'DAN MUBARAK! HAKIKA ALLAH YA GIRMAMAKA (YAYI MAKA KARAMCI) KAMAR YADDA KA GIRMAMA MAHAIFIYAR MARAYUN NAN. KUMA ALLAH YA RUFA MAKA ASIRI KAMAR YADDA KA RUFA ASIRIN MARAYUN NAN".

"HAKIKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI WANI MALA'IKA NE DA SIFFARKA. YA KASANCE YANA TAFIYA TARE DA ALHAZAN GARINKU AWAJEN GUDANAR DA AYYUKAN HAJJI".

"KUMA HAKIKA ALLAH YA BAMA KOWANNE ALHAJI LADAN AIKIN HAJJI GUDA 'DAYA NE. AMMA KAI KUMA ALLAH YA RUBUTA MAKA LADAN AIKIN HAJJI GUDA SABA'IN!!".

Allahu Akbar!! Ya jama'a kunji fa!!!. Ya ku masu alfahari da yawan aikin Hajji!! (Nayi arfa sau kaza! Naje Umrah sau kaza!! Nayi dawafi sau kaza!!).

In dai yardar Allah kuke nema, ku zagaya gidajen Marayu da Miskinai da Fakirai mana! Zaku samu yardar Allah anan!! 

Ka kwashi Matanka da Qananan 'ya'yanka ka tafi dasu Umrah alhali Makwabcinka ko limamin masallacin Unguwarku, ko 'yan uwanka suna kwana da yunwa.. (Wallahi ba lallai ne Allah ya karbi Umrar taku ba). 

Wallahi ladan ciyar da Mayunwata guda goma yafi ladan zuwa Umrarka. Wasu daga cikin magabata suna cewa :



Taskar asirai malam tv AL falaki tv Ramli da hisabi tv Mafarkinka sirrinka tv Gudun duniya tv Domin Karin bayani Sai a turo SAKO ta nombarmu ko email zamu baku amsa 👇🤳 taskaasirai@gmail.com 08124763287 08144698283

Domin samun mustajaba a kwana 9

 Khatimin Allahu Muhammadu  idan ka buga adadin Allahu sau Allahu 66×66=4356 sannan sunan Muhammadu sau  92×92=8464 4356+8468=12820 Ana rubu...